Babban dan Sarkin Musulmi ya yi hadarin mota

Babban dan Sarkin Musulimi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, mai suna Usman Sa’ad Abubakar, wanda aka fi sani da Amir ya hadu da mummunan hadarin mota a ranar Lahadin da ta gabata, tare da wadansu mutum biyu. A lokacin da Majalisar Sarkin Musulmi ta tabbatar da faruwar hadarin, ta bayyana cewa, “Majalisar Sarkin Musulmi tana juyayin […]

Babban dan Sarkin Musulmi ya yi hadarin mota
Babban dan Sarkin Musulmi ya yi hadarin mota

Babban dan Sarkin Musulimi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, mai suna Usman Sa’ad Abubakar, wanda aka fi sani da Amir ya hadu da mummunan hadarin mota a ranar Lahadin da ta gabata, tare da wadansu mutum biyu.

A lokacin da Majalisar Sarkin Musulmi ta tabbatar da faruwar hadarin, ta bayyana cewa, “Majalisar Sarkin Musulmi tana juyayin sanar da al’umma cewa Usman Sa’ad Abubakar da aka fi sani da Amir yanzu haka yana kwance a asibiti, sanadiyar raunin da ya samu a hadarin mota da ya auku da shi tare da dan uwansa Khalifa Muhammad Maccido da Zainab Bara’u Isah a ranar Lahadin da ta gabata, Yanzu suna kan karbar magani.”  

Takardar sanarwa daga fadar da aka raba wa manema labarai, da Sakataren Majalisar Umar Faruk Ladan ya sanya wa hannu ta ci gaba da cewa: “Tun bayan aukuwar hadarin, Sarkin Musulmi da iyalansa da dangi gaba daya suna ta karbar jaje da fatan samun lafiyar yaran, da ke samun kulawar da ta dace a asibiti.” 

Kakakin Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa a Sakkwato, Aliyu Kanya Garba ya kara wa Aminiya bayani kan hadarin, inda ya ce, “Hadarin ya faru ne da misalin karfe 11:35 na safe a kan hanyar Sakkwato zuwa Jega, a Unguwar Bado kusa da gidan man Zamson. Yaran sun samu hadarin ne saboda mummunan gudu, a lokaci guda kuma direban yana amsa kiran waya, sai motar ta kwace ta jefar da su. Sun samu mummunan raunuka, su ukun, maza biyu da mace daya.”

“Bayan al’amarin ya faru aka kira mu muka dauki yaran zuwa asibiti, amma babu hasarar rai,” Kanya.

Da wakilinmu ya ziyarci Asibitin Koyarwa na Usman danfodiyo da ke Sakkwato, inda aka kwantar da yaran, ya iske suna cikin halin jinya, ba su san ma halin da suke ciki ba. Macen ce kawai ta farfado, ita kuma ba ta iya Magana ba har zuwa kammala wannan rahoto.