Babban Janar na sojan Chana ya rataye kansa saboda rashawa
A ranar Talatar da ta gabata ne wani babban Janar na sojan kasar Chana, Zhang Yang ya rataye kansa a gidansa bayan da ya zama babban jigon gwamnati na farko da aka samu da laifin cin hanci da rashawa a tsawon mulkin Shugaba di Jinping a kasar. Zhang Yang wanda shi ne Babban Daraktan Hukumar […]

A ranar Talatar da ta gabata ne wani babban Janar na sojan kasar Chana, Zhang Yang ya rataye kansa a gidansa bayan da ya zama babban jigon gwamnati na farko da aka samu da laifin cin hanci da rashawa a tsawon mulkin Shugaba di Jinping a kasar.
Zhang Yang wanda shi ne Babban Daraktan Hukumar Soji na Harkokin siyasa a kasar ta Chana, ana bincikensa ne bisa zargin sa hannu cikin wadansu badakaloli guda biyu, lamarin da kenan ake ganin ya jawo rataye kansa da ya yi a gidansa kamar yadda jaridar dinhua news agency ta kasar ta bayyana.
Binciken cin hanci da rashawar da ake masa yana da nasaba ne da wata babbar badakala da ta hada da manyan shugabannin Jam’iyyar Komunist da kuma manyan jami’an sojin kasar da ta kai kimanin Dala Miliyan daya da rabi tun a shekarar 2012.
Jaridar ta dinhua ta ruwaito cewa an samu Zhang ne da laifin sanya hannu kan wata takarda da ta sabawa ka’idojin ayyukan ofishin nasa kana kuma ta saba wa dokar kasar, tare da karbar rashawa sannan kuma da mallakar wadansu kadarorin da ya gaza gamsar da hukumomi yadda ya mallake su.
A wata sanarwa da hukumar People’s Liberation Army Daily ta buga a shafinta na twitter, ta bayyana cewa babban janar din ya rataye kansa ne saboda gudun fuskantar hukunci kan zargin da ake ma sa.
“Mun yi mamakin yadda babban jigo na soja irin wannan zai zabi karar da rayuwarsa ta wannan hanya,” a cewar sanarwar.
Haka kuma sanarwar ta ambaci Janar Zhang a matsayin wani mutum ne mai fuska biyu, wanda a kullum yake furta kalaman da’a ga kasar, amma yake cin manarta a karkashin teburinsa. “Rundunar sojanmu ta tanadi manyan bingogi da alburusai masu yawan gaske, don haka ba za ta yi sake wajen boye ko rufa asirin wani mai laifi a kasar ba.”
Janar Zhang dai ya kulla wata mummunar alaka ce da wasu manyan jami’an sojin kasar, Guo Bodiong da kuma du Caihou wadanda tuni aka kore su daga aiki. Guo, kuma shi ne Mataimakin Shugaban hukumar sannan ya kasance babban jami’in (PLA), wanda aka samu da hannun cikin wata mummunar badakalar cin hanci da rashawa, inda aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai a shekarar 2016. Yayin da shi kuma du ya mutu sakamakon cutar sankara a lokacin da ake tsaka da bincikensa a 2015.