Babban Kifi ya kashe wani mutum a gabar Tekun Maliya

An hana ninkaya da sauran harkokin wasanni a wurin na kwana biyu.

Babban Kifi ya kashe wani mutum a gabar Tekun Maliya

Wani shirgegen kifi ya kashe wani dan Rasha a kusa da wurin shakatawa na Hurghada da ke gabar Tekun Maliya a Masar.

Mutumin ya gamu da ajalinsa ne da tsakar ranar Alhamis, a cewar hukumomin Rasha da Masar, yayin da yake ninkaya a ruwan.

Wani da abin ya faru a kan idonsa ya nade shi a bidiyo kuma ya bai wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters.

Bidiyon ya nuna matashi mai shekara 23 mai suna Vladimir Popov yana dirango a ruwa kafin daga baya a janye shi zuwa kasan ruwa.

A cewar Reuters, wani mai ninkaya ya bayyana yadda wani mai aiki a wurin ya yi yekuwa a wani otel da ke kusa kuma mutane suka yunkuro don ceto shi, amma ba su iya kaiwa gare shi a kan lokaci ba.

Tun daga ranar Juma’a dai aka hana ninkaya da sauran harkokin wasanni a wurin na kwana biyu, kamar yadda Ma’aikatar Kula da Muhalli ta Masar ta bayyana.

Wata tawagar kwararru ta kama kifin da ake kira shark a Turance kuma suna tantance shi da zimmar gano musababin kai wa mutumin hari, in ji ma’aikatar

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume