Babban layin lantarki ya ɗauke karo na 4 cikin mako guda
Lalacewar babban layin wutar lantarki sau uku a mako guda ya fusata ’yan Nijeriya
Wutar lantarkin Najeriya na ci gaba da samun koma baya sakamakon lalacewar babban layin lantarki na ƙasa a safiyar ranar Asabar.
Matsalar ta jefa miliyoyin ’yan ƙasar cikin duhu.
- Shin darasi ne Isra’ila ta ɗauka daga yaƙin 2006 da Hezbollah?
- Tarihin sarautar Dan-Isa a Masarautar Zazzau
Wannan dai shi ne karo na huɗu da babban layin wutar lantarkin ke lalacewa cikin mako guda, kuma karo na takwas a 2024.
Bayanai sun nuna cewa babu ko megawatt ɗaya a babban layin zuwa a safiyar Asabar.
Masana harkar wutar lantarki dai sun yi kira da a sabunta kayayakin babbar cibiyar wutar a Najeriya.
Sun ce yawan lalacewar wutar lantarkin da ake samu na da alaƙa ne da tsufan kayayyakin babbar cibiyar lantaki ta ƙasa.
Yanzu haka dai, ’yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan katsewar babban layin wutar lantarkin a kafafen sada zumunta.
Lamarin dai ya zama babban batun muhawara a wannan makon.