Babban layin lantarkin Arewa ya sake ɗaukewa
A halin yanzu yankuna a Arewacin Nijeriya suna cikin duhu, sakamakon lalacewar babban layin da ke kai lantarki zuwa yankin.
Babban layin wutar lantarkin da ke kawo wuta Arewacin Nijeriya ya sake ɗaukewa.
Babbar Manajan Hulɗa da Jama’a ta Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Najeriya, Ndidi Mbah, ta ce sanar da hakan a safiyar Talata.
Sanarwar ta bayyana cewa wutar ta sake daukewa ne a ranar Lahadi, kasa a awa 24 bayan gyara layin a sakamakon daukewar da ya yi a ranar Lahadi.
Ta bayyana cewa a halin yanzu akasarin yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma na cikin duhu, da wani yankin na Arewa ta Tsakiya.
- Diyyar N100bn: Matatar Ɗangote ta janye ƙarar da ta maka NNPCL
- Ɓarayin “One chance” sun kashe matashiya a Abuja
- NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da CNG
“Currently, TCN has restored supply to the 132kV transmission line from New Haven to Apir, but the 330kV lines remain out of service, impacting power supply in the Northern region of the country. Sadly, the TCN Shiroro-Mando transmission line is also down due to security reasons, causing power outage in the North.”
Karo na biyar da babban layin wutar lantarkin ke yake lalacewa cikin mako biyu a Najeriya.
Mbah ya sanar da cewa manyan layukan wuta na 1 da na 2 da suka ƙarfin 330kv da suka tashi daga Ugwaji zuwa Apir, sun katse, kuma ana halin yanzu ana gudanar da bincike domin gano hakikanin inda matsalar take.