Babban layin lantarkin Najeriya ya faɗi karo na 12 a 2024
Dukkanin tashoshin da ke rarraba wutar sun daina aiki tun daga ƙarfe 2 na rana.
Babban Layin Wutar Lantarkin Najeriya, ya sake faɗuwa karo na 11 a shekarar 2024.
Wannna na cikin wata sanarwa da Hukumar Gudanar da Tsarin Wutar Lantarki ta Ƙasa (ISO), reshen Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), ta fitar.
- Boko Haram sun fille kan masunta 14 a kan iyakar Najeriya
- Shugaban Karamar Hukumar Katcha ta Jihar Neja ya rasu
Ta ce dukkanin tashoshin da ke rarraba wutar sun daina aiki tun daga ƙarfe 2 na rana.
Kafin haka, misalin karfe 1 na rana, tashoshin suna samar da kimanin megawatt 3,087 na wutar lantarki.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Jos (Jos Disco), ya tabbatar da faruwar matsalar cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce: “Rashin wutar lantarkin da ake fuskanta a yankunanmu ya faru ne sakamakon katsewar wuta daga babban layin rarraba wuta ta ƙasa.
“Wannan katsewa ta faru ne a ranar Laraba, 11 ga wata Disamba, 2024, da misalin ƙarfe 1:33 na rana, wanda ya haifar da rashin wuta a dukkanin manyan layukanmu.”
Sanarwar ta ƙara da cewa: “Muna aiki tuƙuru domin gyara wutar lantarki yadda ta ke a baya. Muna godiya da haƙurinku da fahimtarku yayin da muke ƙoƙarin yi muku hidima.”
Idan ba a manta ba, a baya an sha fuskantar irin wannan matsala idan wutar lantarki ke ɗaukewa gaba ɗaya a faɗin Najeriya.
Irin wannan ta faru a baya-bayan nan, inda aka ɗauke wa Arewacin Najeriya wutar lantarki gaba ɗaya, har na tsawon wajen mako biyu, lamarin da ya janyo asarar miliyoyin dukiya.