Babban layin wutar lantarki ya faɗi karon farko a 2025
A shekarar 2024 sau 12 babban layin wutar na ɗaukewa, lamarin da ya jefa miliyoyin jama’a cikin duhu.
Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa.
Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa.
- Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda
- Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi
Cikin wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya fitar a shafinsa na X, ya bayyana cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar ranar Laraba.
Sai dai AEDC, ya ce ana aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawo da wutar da zarar an shawo kan matsalar.
Rahotanni, sun nuna cewa yawan wutar lantarki a kan babbar tashar wutar lantarki ta ƙasa (TCN), ya ragu daga megawat 4,064.70 da misalin ƙarfe 11 na safe zuwa megawat 1,222.78 da ƙarfe 12 na rana.
“Muna mai baƙin ciki da sanar da ku cewa wata matsala ta auku a babban layin wuta na ƙasa da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar yau, wanda ya haddasa ɗaukewar wuta a yankunanmu.
“Duk da cewa an fara dawo da wuta a hankali, muna tabbatar muku cewa muna aiki tare da hukumomin da suka dace domin maido da wutar gaba ɗaya da zarar an daidaita layin.
“Muna godiya da fahimtarku da haƙurin da kuke yi yayin da muke ƙoƙarin inganta ayyukanmu a gare ku.”
Babban layin lantarki na Najeriya na fuskantar matsalolin faɗuwa akai-akai, musamman a shekarar da ta gabata, inda hakan ke haddasa matsalolin ɗaukewar wuta a faɗin ƙasar.
Wannan na zuwa ne bayan da Najeriya ta fuskanci faɗuwar layin wutar lantarki sau 12 a shekarar 2024.