Babban Limamin Abeokuta ya kwanta dama
Babban limamin lardin Egba a jihar Ogun, Sheik Liadi Orunsolu ya riga mu gidan gaskiya. Allah Ya yi wa Sheik Orunsolu rasuwa ne a gidansa da ke Abeokuta da sanyin safiyar Talata, 26 ga watan Mayu bayan ya dade yana fama da rashin lafiya da ke da alaka da tsufa ko yawan shekaru. A lokacikin […]
Babban limamin lardin Egba a jihar Ogun, Sheik Liadi Orunsolu ya riga mu gidan gaskiya.
Allah Ya yi wa Sheik Orunsolu rasuwa ne a gidansa da ke Abeokuta da sanyin safiyar Talata, 26 ga watan Mayu bayan ya dade yana fama da rashin lafiya da ke da alaka da tsufa ko yawan shekaru.
A lokacikin rayuwarsa, Sheik Liadi Orunsolu shi ne jagorantar lardin ya da ya hadar da Birnin Abeokuta da wasu sassan jihar.
- Mahaifin Babban Editan Daily Trust ya rasu
- Tsohon Ministan lafiya Dakta Haliru ya rasu
- Fitattun mutum 10 da suka rasu cikin mako daya a mace-macen Kano
Aminiya ta gano cewa Shehun malamin ya kwanta jinya a wannan karon tun gabanin watan azumin Ramadan.
Za kuma a yi masa sutura, a binne shi da misalin karfe 4 na yamma a ranar Talatar bisa tsarin addinin Islama.