Babban Limamin Ghana ya bukaci fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban
Babban Limamin kasar Ghana Sheikh Dokta Osman Nuhu Sharubutu ya Jinjinawa matsayin fahimtar juna da ke tsakanin addinai daban-daban na Ghana abin da ya ce ya kamata kasashe makwabta su yi koyi da shi . Sheikh Sharubutu ya yi wannan kira ne a wurin wani taron gode wa Allah da Limaman coci suka shirya a […]
Babban Limamin kasar Ghana Sheikh Dokta Osman Nuhu Sharubutu ya Jinjinawa matsayin fahimtar juna da ke tsakanin addinai daban-daban na Ghana abin da ya ce ya kamata kasashe makwabta su yi koyi da shi .
Sheikh Sharubutu ya yi wannan kira ne a wurin wani taron gode wa Allah da Limaman coci suka shirya a dandalin ’Yanci wato Independence Skuare a Accra, a makon jiya. An shirya taron ne domin gode wa Allah game da zaman lafiya da aka samu Ghana gabanin babban zaben kasar a shekarar 2012, lokacin da ake yin zaben da bayan zaben har lokacin da abokan adawa suka kalubanci sakamakon zaben ,aka tafi kuto, kuma ta bayar da sakamakonta duk da haka aka zauna lafiya. Lalle wannan ya isa a gode wa Allah.
Taron na yini guda ya samu halartar mabiya addinin Kirista da Musulmi har shagabanin mabiya addinan gargajiya . Har ila yau, an yi wa kasa da shugaban kasa da ministotinsa da al’ummar Ghana addua’a. Hakazalika, an yi addu’ar musamman dangane da zaman lafiya da tsaron nahiyar Afirka da kuma neman kariyar Ubangiji game da cutar Ebola.
Sheikh Sharubutu ya bayyana farin cikinsa musanman game da yadda Musulmi da Kirista ke zama tare lami lafiya,abin da ya ce ya isa abin koyi ga sauran jama’a da ke zaune a sauran kasashe.