Babban Limamin Minna Sheikh Isa Fari ya rasu

Babban Limamin birnin Minna da ke Jihar Neja,Sheikh Isah Ibrahim Fari ya riga mu gidan gaskiya. Sheikh Fari wanda ya shafe fiye da shekaru 20 a matsayin Babban Limamin Minna ya rasu ne a ranar Asabar da daddare a Asibiti Ƙwararru na IBB da ke Minna. Gwamnan Neja, Mohammed Umar Bago ya bayyana alhinin dangane […]

Babban Limamin Minna Sheikh Isa Fari ya rasu

Babban Limamin birnin Minna da ke Jihar Neja,Sheikh Isah Ibrahim Fari ya riga mu gidan gaskiya.

Sheikh Fari wanda ya shafe fiye da shekaru 20 a matsayin Babban Limamin Minna ya rasu ne a ranar Asabar da daddare a Asibiti Ƙwararru na IBB da ke Minna.

Gwamnan Neja, Mohammed Umar Bago ya bayyana alhinin dangane da rasuwar Babban Limamin wanda ya shafe shekaru 93 a doron ƙasa.

Cikin sanarwar da Babban Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Neja, Bologi Ibrahim ya fitar, ya bayyana rasuwar Sheikh Isah Fari a matsayin babban rashi ga jihar da kuma ilahirin al’ummar Musulmi.

Ya bayyana marigayi Sheikh Isah Fari a matsayin mutum wanda ya kai ƙololuwa wajen tawali’u kuma jakadan zaman lafiya wanda ya shafe rayuwarsa wajen yaɗa da’awar addinin Islama ta hanyar ƙaunar juna da sadaukarwa.

Yayin da yake jajanta wa Masarautar Minna, iyalansa da dukkan al’ummar Musulmi, Gwamna Bago ya yi addu’ar Allah Ya yi wa mamacin sakamako da Aljannar Maɗaukakiya.

Aminiya ta ruwaito cewa za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 2:00 na ranar Lahadin nan a Babban Masallacin Minna.

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta

Jerin Manyan Dambarwan Kano a 2024