Babban Mai shari’a Dahiru Musdapha (1942 zuwa 2018)

Daya daga cikin mashahuran masu shari’a, Mai shari’a dahiru Musdapha ya rasu ranar 22 ga Janairun 2018 yana da shekara 75. Ya rasu ne a asibitin Landan, inda ya yi fama da jinya. Musdapha ya yi aiki tuquru, inda ya samu daukaka a aikinsa na shari’a, al’amarin da ya kai shi ga zama babban mai […]

Babban Mai shari’a Dahiru Musdapha (1942 zuwa 2018)

Daya daga cikin mashahuran masu shari’a, Mai shari’a dahiru Musdapha ya rasu ranar 22 ga Janairun 2018 yana da shekara 75. Ya rasu ne a asibitin Landan, inda ya yi fama da jinya. Musdapha ya yi aiki tuquru, inda ya samu daukaka a aikinsa na shari’a, al’amarin da ya kai shi ga zama babban mai shari’a na Najeriya a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2012.

An haife shi a garin babura da ke Jihar Jigawa ranar 15 ga yulin 1942, ya yi karatunsa a Jami’ar Ahmadu Bello da Cibiyar bincike kan harkokin Afirka ta SOAS a Landan. Ya halarci makarantar qwarewa  ta lauyoyi a shekarar 1968. Ya yi aiki a amtsayin Alqalin alqalan Jihar Kano a tsakanin shekarun 1979 zuwa 1985. Musdapha ya yi aiki a kotun daukka qara a tsakanin shekarun 1985 zuwa 2003. Likafarsa ta yi gaba zuwa alqalin kotun qoli a shekarar 2003, sannan aka nada shi babban mai sharia na qasa a ranar 27 ga Agustan 2011, inda ya gaji Cif Joji Aloyisius Katsina-Alu. Shi ma Musddapher daga bisani Babbar mai shari’aAloma Mariam Mukhtar ce ta gaje shi a shekarar 2012.

Musdapha ya zama Babban mai shari’a na qasa a daidai lokacin da qimar hukumar shari’a ta yi qasa warwas, sakamakon rikicin da aka tafka tsakanin Cif joji Katsina-Alu da tsohon shugaban Kotun daukaka qara Maishari’a Ayo Salami da aka dakatar da shi. A dan taqaitaccen wa’adin jan ragamarsa babban mai shari’ar na qasa, ya yi aiki tuquru wajen dawo da martabar hukumar shari’a, sannan ya ajiye aiki a shekarar 2012 lokacin da ya cika shekara 70 da haihuwa.

Shugaba Buhari ya yi ta’aziyya ga masarautun Kano da Ringim da qwararrun abokan aikinsa da ’yan uwa da abokan arzikin mashahurin alqalin da ya bayar da gudunmuwarsa wajen tsarawa da jerantawa don bunqasa kundin tsarin mulkin qasar nan da harkokin shari’a, al’amuran da suka sanya za a yi ta tunawa da matuqar yaba masa. Shugaban qasa ya yi nuni da irin tsarin jagorancin Musdapha a lokacin ayyukansa, wadanda suka hada da Kwamishinan Shari’a na Jihar Kaduna  da kuma kasancewarsa shugaban daukacin kotunan daukaka qara da ta qoli.

Mai shari’a Misdapher, shi ne wanda da kama ragamar shugabancinsa, sai ya kafa kwamitin mutum 28 masu ruwa da tsaki, wadanda suka hada da tsofaffin cif joji-joji da tsofaffin shugabannin kotun daukaka qara da alqalan kotun qoli da suka yi ritaya tare da manyan lauyoyin qasar nan. Kwamitin ya kasance qarqashin jagorancin tsohon babban mai shari’a na Najeriya, Mai shari’a Muhammad Lawal Uwais. An dora wa kwamitin alhakin warware matsaloli da ingancin shari’o’in da ba a gudanar da su kan lokaci da rashin managrcin tsari da rashin ingantattun kayan aiki, tattare da yanayin aiki mara kyau ga jami’an shari’a da wadanda ke taima musu. Sannan an dora masa alhakin shawo kan qarancin ilimin yanke hukunci da cin hanci da rashawa, sannan da illar tasirin masu yin katsalandan don cimma wata manufa ta siyasa, al’amuran da suka rikirkita harkokin shari’a da bata musu suna.

Mai shari’a Musdapha ya yi qoqarin aiwatar da managarcin gyara, snanan ya buqaci a sake bin Kadin nazarin kundin tsarinm mulki game da manyan kotuna da aka tattara bayanai kansu da kuma qananan kotuna, al’amarin da ya hada da sake fasalin da inganta hukumar shari’a ta NJC da Hukumar Shari’a ta Tarayya (FISC) da Cibiyar Nazarin Harkokin Shari’a ta NJI) duk da manufar kawo gyar aa harkokin shari’a, da bullo da tsarin sabuntawa ta yadda za a dawo da martaba da qimar darajar hukumar shari’a mara aibu. Marigayi Mai shari’a ya yi fafutikar qirqiro da hukuma maizaman kanta sabanin Hukumar shari’a ta NJC don ladaftarwa da sauke alqalai daga muqamansu. Ya gabatar wa Majalisar qasa, sannan ya buqaci a amince da qudurin gyare-gyare 47 da suka shafi shari’a a matsayin wani bangare na gyaran harkokin shari’ar.

Ya kasance mai fafutikar ganin an riqa yin tsarin karba-karbar shugabancin qasa, sannan Mai shari’a Musdapha ya fafata wajen yaqi da cin hanci da rashawa da keta haddin doka, al’amuran da suka dabaibaye harkokin shari’a da kafafen yada labarai, kuma ya nuna matuqar adawarsa da ta’addanci, al’amarin da a cerwarsa, ya dauki wani mummunan salo.

Marigayin ya bar matarsa da ’ya’ya uku, wadanda daga cikinsu akwai Hadiza dahiru Musdapha, wata alqalin kotun Majistare da Kaloma Musdapha, mataimakin kan harkokin yada labarai ga Gwmanan Jigawa, Badaru Abubakar. Mun samu natsuwa ganin yadda Babban mai shari’a na Najeriya dahiru Musdapha a rayuwarsa ya yi kira ga daukacin alqalan Najeriya da su yunqura wajen shawo kan daimbin qalubalen da ke munana su, ta hanyar sake fasali da qwarin gwiwar a harkokin shari’a. Ya rayu managarciyar rayuwa mai tasiri, kuma abin koyi da ya cancanci a yi koyi da shi. Allah Ya ba shi aljannar Firdausi.