Babban sako ga ilahirin Gizagawan Najeriya

An dauki lokaci mai dan tsawo da ba a ji duriyar kungiyar Gizagawan Najeriya ba. Wannan kuwa bai rasa nasaba da gyare-gyare da kintse-kintse da aka dauki lokaci ana gudanarwa ba, domin ganin an samu saiti da dora kungiyar kan gwadabe na kirki. Babban kudurin dai shi ne, jaddada zumunci tsakanin juna, fadakarwa, tunatarwa da […]

Babban sako ga ilahirin Gizagawan Najeriya

An dauki lokaci mai dan tsawo da ba a ji duriyar kungiyar Gizagawan Najeriya ba. Wannan kuwa bai rasa nasaba da gyare-gyare da kintse-kintse da aka dauki lokaci ana gudanarwa ba, domin ganin an samu saiti da dora kungiyar kan gwadabe na kirki. Babban kudurin dai shi ne, jaddada zumunci tsakanin juna, fadakarwa, tunatarwa da taimakon juna. A yanzu al’amari ya daidaita, an samu sababbin shugabannin da za su ci gaba da tafiyar da kungiyar, bisa jagorancin jajirtaccen mutum da ake wa inkiya da “Agogo Sarkin Aiki” Malam M. K. Adam Gombe. A yanzu wannan shugaba tare da mukarrabansa sun shirya tsaf, don haka ga babban sako nan ga ilahirin Gizagawa, maza da mata daga bakinsa: 

 

Assalamu alaikum Gizagawa. Ina fatan kuna halin lafiya da iyalanku baki daya. Marasa lafiyar cikinmu, Allah Ya ba su lafiya, amin.

Babban abin da ya kai ni ga ambata wadancan kalaman da ke sama shi ne, tunatarwa domin da tunatarwa ne za mu gane har mu gamsu da juna. Babu shakka Musulunci kansa nasiha ne kuma tutarwa ne.

Zan iya tunawa a lokacin da nake neman kuri’unku, da dama daga cikinku sun yi mani alkawarin cewa bayan kada kuri’a za su ba da hadin kai da goyon baya, in sha Allah.

Saboda haka, ku fa sani, ba zan samu damar gudanar da aiki ba, ba tare da hadin kai da goyon bayanku ba. Na san akwai uzuri, akwai yanayi, akwai juriya da hakuri. Saboda haka na dauki uzuri da yanayi, abin da ya rage maku shi ne juriya da hakuri; wannan kuma da ni da ku za mu daure mu kai zuwa inda Allah Ya so!

A karshe, ina kara jawo hankalinmu da cewa, mu sani idan na gaza wajen cika alkawarin da na dauka, kada kowa ya zarge ni, ya fara tambayar kansa, ta ina ya gaza?

Ina godiya matuka da irin shawarwarinku da na ke samu. Sai dai fa ku sani, shawara ba ta aiki ita kadai, musamman a wannan yanayi da muke.

Muna nan dauke da sabbin tsare-tsare da kudurori masu amfani a wannan kungiya ta mu mai albarka.

Allah Ya taimake mu, Ya ba mu ikon sauke nauyin da muka dauka.

Na gode!

Naku M. K. Adam, Shugaban kungiyar Gizago na kasa (GZG-023-GMB)