Babbar Jojin Najeriya na yunkurin jingine ka’ida wajen nada Shugaban Kotun daukaka kara

An tashi taron Majalisar Harkokin Shari’a ta kasa baram-baram a farkon wannan wata, bayan yunkurin da Babbar Jojin Najeriya Maryam Aloma Mukhtar ta yi yunkurin ajiye dukkan manyan alkalan Kotun daukaka kara wajen nada magajin tsohon Shugaban Kotun Mai shari’a Isa Ayo Salami, kamar yadda Aminiya ta samu labari a ranar Litinin. Mai shari’a Salami […]

Babbar Jojin Najeriya na yunkurin jingine ka’ida wajen nada Shugaban Kotun daukaka kara

An tashi taron Majalisar Harkokin Shari’a ta kasa baram-baram a farkon wannan wata, bayan yunkurin da Babbar Jojin Najeriya Maryam Aloma Mukhtar ta yi yunkurin ajiye dukkan manyan alkalan Kotun daukaka kara wajen nada magajin tsohon Shugaban Kotun Mai shari’a Isa Ayo Salami, kamar yadda Aminiya ta samu labari a ranar Litinin.
Mai shari’a Salami wanda aka dakatar da shi tun shekarar 2011, ya yi ritaya daga aiki a watan Oktoban da ya gabata, inda ya bude hanyar nada magajinsa. Sai dai Aminiya ta samu labari daga majiya mai tushe a bangaren shari’a cewa Mai shari’a Mukhtar ta mika bukatar a nada Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun wata karamar alkali a Kotun koli a matsayin Shugabar Kotun daukaka kara.
Mai shari’a Kekere-Ekun, wadda ta fito daga Jihar Legas alkali ce a Kotun daukaka kara kafin a tura ta Kotun koli watanni shida da suka gabata.
Idan da Babbar Jojin ta samu nasara, za ta yi waje da manyan alkalan Kotun daukaka karar, wadanda suka kunshi mafi girma a cikinsu Mai shari’a dalhatu Adamu wanda ya yi riko na wata 15 bayan dakatar da Salami. Sai mai bi masa wajen girma kuma mai rikon Kotun daukaka karar a yanzu Mai shari’a Zainab Bulkachuwa. Mai shari’a Amiru Sanusi, Shugaban Kotun daukaka kara ta shiyyyar Abuja shi ne na uku a girma, yayin da Mai shari’a Ja’afaru Mika’ilu yake na hudu, sai Mai shari’a Amina Augie ta biyar a cikin alkalan Kotun daukaka karar.
Aminiya ta samu bayanin cewa Hukumar Harkokin Shari’a ta Tarayya ta ba da sunan alkalai mafiya girma ga Majalisar Shari’a domin ta zabi daya daga cikinsu tare da ba Shugaban kasa Goodluck Jonathan domin nada shi Shugaban Kotun daukaka karar, amma taron Majalisar Shari’ar ya tashi baram-baram lokacin da Babbar Jojin ta so ta jingine dukkan mutum uku da aka zaba.
Majiyoyin sun ce wakilan Majalisar Shari’ar sun fice daga taron suna masu rashin amincewa, inda suka nace cewa dole a bi ka’idar girma da aka saba.
Tun kirkiro Kotun daukaka kara a 1976 girma ake dubawa wajen nada shugabannin kotun. Haka ita ma Kotun kolin akan nada shugabanta ne bisa lura da alkali mafi girma a tsakanin alkalanta har aka zo kan Mai shari’a Maryam Mukhtar.   
Tuni wani lauya mai zaman kansa ya rubuta takardar korafi ga Babbar Jojin yana kiranta cewa kada ta kauce wa tsarin na nada alkali mafi girma lokacin nada Shugaban Kotun daukaka karar.
Lauyan Barista Sanusi Musa na rukunin gidaje na Kado da ke Abuja ya tunatar da Babbar Jojin cewa “Majalisar Shari’a a kwanakin baya a ki amincewa da zabar wadanda za a nada a matsayin manyan alkalan jihohin Ribas da Adamawa da Kwara da Osun bisa hujjar an keta ka’idar nan a nada alkali mafi girma. Gwamnonin wadancan jihohi bisa ikon da tsarin mulki ya ba su, sun mika sunayen wadacan alkalai a matsayin wadanda za su nada a mukaman manyan joji a jihohinsu, amma Majalisar Shari’a a karkashin jagorancinki ta tsaya kan bakanta tare da shawartar gwamnonin su sake tura sunayen alkalan da suka fi girma a manyan kotunan jihohinsu domin nada su.”
Barista Sanusi ya tunatar da Babbar Jojin cewa ba ta ji dadi ba a 1979 lokacin da aka daukaka Mai shari’a dahiru Musapha a kanta domin ya zama Babban Jojin Jihar Kano. Ya bukaci kada ta yi wa abokan aikinta irin abin da bai yi mata dadi ba wajen zaben magajin Salami.
Wata majiyar shari’a ta shaida wa Aminiya cewa Mai shari’a Kekere-Ekun tana kasa da alkalai tara na Kotun daukaka karar. Majiyar ta ce nada ta a Kotun koli ya faru ne sakamakon tsarin raba-daidan mukamai amma ba bisa girma, kuma wannan ne ya sanya aka daukaka ta zuwa Kotun kolin. Ya ce, da za ta dawo Kotun daukaka kara a matsayin shugabanta, hakan zai haifar da rikici tare da kawo wahala wajen gudanar da harkokin kotun.
Kakakin Majalisar Shari’a Mista Soji Oye ya ki cewa komai lokacin da Aminiya ta tuntube shi domin jin ta bakinsa. Shi kuma Babban Sakataren Majalisar Shari’a Halilu danladi an kasa samunsa.