Babbar Kotun Pakistan ta ba da umarnin sakin tsohon Shugaban kasar
A shekaranjiya Larabar ce wata Babbar Kotu a kasar Pakistan ta soke hukuncin zaman gidan yari da aka yanke wa tsohon Firayi Ministan kasar, Nawaz Sharif da ’yarsa Maryam da kuma surukinsa Kyaftin Muhammad Safdar. Matakin kotun ya shafi wata shari’a ta cin hanci da rashawa da ake tuhumar mutanen ukun da mallakar wasu gidajen […]

A shekaranjiya Larabar ce wata Babbar Kotu a kasar Pakistan ta soke hukuncin zaman gidan yari da aka yanke wa tsohon Firayi Ministan kasar, Nawaz Sharif da ’yarsa Maryam da kuma surukinsa Kyaftin Muhammad Safdar.
Matakin kotun ya shafi wata shari’a ta cin hanci da rashawa da ake tuhumar mutanen ukun da mallakar wasu gidajen kasaita guda hudu a birnin Landan, wadanda suka kasa bayyana yadda suka mallake su.
Gidan talabijin na ARY News ya sanar a ranar Larabar cewa, ya Babbar Kotun Islamabad ta ce a saki Nawaz Sharif da Maryam Nawaz da kuma Kyaftin Muhammad Safdar daga kurkuku.
Wannan hukuncin dai na zuwa ne a daidai lokacin da wata kotu ke sauraren daukaka karar da lauyoyin Mista Nawaz suka shigar a wata kotun ta daban, a kan shari’ar da aka fi sani da ‘Badakalar Abenfield,’ wato batun cin hanci da rashawa na gidajen Abenfield.
A baya kotu ta same su da laifuffukan da ake zarginsu da su, inda ta daure Nawaz Sharif shekara 11 a gidan yari, yayyin da ta daure ’yarsa Maryam Nawaz shekara 7, sai Muhammad Safdar aka daure na tsawon shekara guda.
Dukansu suna zaman gidan kaso a halin da ake ciki, amma za a sake su bayan sun cika wasu sharudda da Babbar Kotun ta Islamabad ta zayyana. Sharuddan sun hada da biyan wasu kudaden ka’ida da mika fasfunan tafiye-tafiyensu ga hukumar ’yan sanda.