Babbar matar Sarkin Ningi ta riga mu gidan gaskiya
Sarkin Ningi ya aure Hajiya Hama tun a shekarar 1952
Allah Ya yi wa uwar gidar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya wato Hajiya Hajiya Hama rasuwa.
Hajiya Hama, wadda Sarkin ya aura tun a shekarar 1952, ta rasu ne tana da shekara 85 a ranar Litinin.
- An yi jana’izar matar Sarkin Katsina, marigayi Alhaji Kabir Usman
- Ana kashe mu saboda tsare Kanu –‘Yan Arewa
Ta rasu ta bar ’ya’ya takwas cikinsu har da Chiroman Ningi, Alhaji Haruna Yunusa da kuma Damburam Ningi, Alhaji Yusuf Yunusa.
Sanarwar rasuwar Hajiya Hama da Masarautar Ningi ta fitar a ranar Talata ta ce an yi janai’zar ta a Fadar Sarkin Ningi a safiyar Talata kamar yadda addinin Islama ya tanadar.