Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta ba makarantu hutun kwana 10

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta ce hutun zai fara ne daga ranar Laraba, 4 ga watan nan na Yuni da muke ciki

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta ba makarantu hutun kwana 10

Gwamnatin Kano ta ba makarantu hutun kwanaki goma domin bikin Babbar Sallah da za a yi ranar Juma’ar wannan makon.

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa makarantun za su fara hutun ne daga ranar Laraba, 4 ga watan nan na Yuni da muke ciki, zuwa ranar Lahadi, 15 ga wata.

Sanarwar ta kuma bukaci iyaye da ’ya’yansu suke makarantun kwana da su je da wuri domin daukar yaran a ranar Laraba.

Kwamishinan mai kula da ma’aikatar, Ali Makoda, ya kuma bukaci iyaye da su tabbata daliban sun dawo makaranta a kan kari bayan kare hutun Babbar Sallar.

A sakonta na taya daliban murna da fatan za a yi Babbar Sallah lafiya, ma’aikatar ilimin ta bayyana cewa hutun ya yi daidai da jadawalin zangon karatu da ake ciki, kuma ba a canza shi ba.