Babbar ’yar Galadiman Dutse ta rasu

An dai haifi marigayiyar a ranar 31 ga watan Mayu a shekarar 1962.

Babbar ’yar Galadiman Dutse ta rasu

Babbar ’yar Galadiman Dutse, Hafsatu Basiru Sanusi ta rasu bayan shafe shekaru 62 a doron ƙasa.

Aminiya ta ruwaito cewa rasuwar Hafsatu ta jefa iyalan Mai Martaba Galadiman Dutse, Alhaji Basiru Muhammad Sanusi cikin jimami.

An dai haifi marigayiyar a ranar 31 ga watan Mayu a shekarar 1962.

Hafsatu ta  kasance mai son jama’a, kulawa da sadaukarwa ga danginta kamar yadda wakilinmu ya ruwaito.

Marigayiyar ta rasu ta bar ’ya’ya huɗu ciki har da Lukman Mahmoud Isah Dutse, ma’aikaci a Babban Bankin Najeriya da kuma Alawiyyah Mahmoud Isah Dutse da ke aiki a Hukumar Kula da Bankuna da Kamfanoni Inshora NDIC.

Sauran ’yan uwanta da suka shiga alhini sun haɗa da Jamilu Basiru Sanusi (Turakin Dutse kuma Hakimin Dutse) da Zahraddeen Basiru Sanusi (Dan’Isah Dutse kuma Hakimin Sakwaya) da Sanusi Basiru Sanusi (Dan Darman Dutse).

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda