Babi na Ashirin da Hudu: Hajjin mace ga namiji ya halatta

Babi na Ashirin da Hudu: Hajjin mace ga namiji ya halatta328. An karbo daga Abdullahi dan Maslamata ya ce: “Daga Malik daga dan Shihab daga Sulaiman dan Yassar daga Abdullahi dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Fadalu ya kasance goye a bayan Annabi (SAW) sai wata mace daga kabilar Kas’am ta zo […]

Babi na Ashirin da Hudu: Hajjin mace ga namiji ya halatta
Babi na Ashirin da Hudu: Hajjin mace ga namiji ya halatta

Babi na Ashirin da Hudu: Hajjin mace ga namiji ya halatta
328. An karbo daga Abdullahi dan Maslamata ya ce: “Daga Malik daga dan Shihab daga Sulaiman dan Yassar daga Abdullahi dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Fadalu ya kasance goye a bayan Annabi (SAW) sai wata mace daga kabilar Kas’am ta zo (wucewa) sai Fadalu ya rika kallonta ita ma tana kallonsa. Sai Annabi (SAW) ya rika kawar da fuskar Fadalu zuwa wani gefe. Sai (matar) ta ce: “Hakika farlancin Allah na Hajji ya fada a kan Babana alhali ya tsufa tukuf bai iya zama kan abin hawa, shin zan iya yi masa Hajji? Ya ce, “Na’ama.” Wannan ya faru ne a Hajjin Ban-Kwana.

Babi na Ashirin da Biyar: Hukuncin Hajjin yara
329. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce: “Hammadu dan Zaid ya ba mu labari daga Ubaidullah dan Abu Yazid ya ce: “Na ji dan Abbas (Allah Ya yarda da su), yana cewa: “Annabi (SAW) ya aike ni zuwa Mina da kayan nauyi daga Jama’a (Muzdalifa) da dare.”

330. An karbo daga Is’hak ya ce: “Yakub dan Ibrahim ya ba mu labari ya ce, dan dan uwana dan Shihab ya ba mu labari daga Baffansa ya ce, Ubaidullahi dan Abdullahi danUtba dan Mas’ud ya ce: “Lallai Abdullahi dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Wata shekara na taho bisa wata jaka lokacin na yi kusan balaga Manzon Allah (SAW) na tsaye yana Sallah a Mina har na bi gaba ga sahun farko, sa’an nan na sauka daga kanta ta rika kiwonta na shiga na yi sahu tare da mutane a bayan Manzon Allah (SAW).” Yunus ya ce, daga dan Shihab cewa: “A Mina ne, lokacin Hajjin Ban-Kwana (ya nuna dan Abbas ya yi Hajji kafin balagarsa).”

331. An karbo daga Abdurrahman dan Yunus ya ce: “Hatim dan Isma’il ya ba mu labari daga Muhammad dan Yusuf daga Sa’ib dan Yazid ya ce: “Babana ya yi Hajji tare da ni da Manzon Allah (SAW) lokacin ina dan shekara bakwai.”

332. An karbo daga Amru dan Zurarata ya ce: “Alkasim dan Malik ya ba mu labari daga Ju’aid dan Abdurrahman ya ce: “Na ji dan Umar dan Abdul’aziz yana cewa ga Sa’ib dan Yazid lallai ya kasance an yi Hajji da shi a cikin madauka kayan Annabi (SAW).”

Babi na Ashirin da Shida: Hajjin mata
Ahmad dan Muhammad ya fada mini, ya ce, Ibrahim ya ba mu labari daga Babansa daga kakansa cewa: “Umar (Allah Ya yarda da shi) ya yi izini ga matan Annabi (SAW) a karshen Hajjin da ya ziyarce ta. Sai ya aika Usmanu dan Affan da Abdurrahman tare da su.”

333. An karbo daga Musaddad ya ce: “Abdulwahid ya ba mu labari ya ce, Habib dan Abu Amrata ya ba mu labari, ya ce: A’isha ’yar dalhat ta ba mu labari daga A’isha Uwar Muminai (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Na ce, ya Manzon Allah! Shin mu mata ba za mu tafi yaki tare da ku ba? Sai ya ce, “Mafificin jihadi kuma wanda ya fi kyawo shi ne Hajji, Kuma Hajjin ya zama karbabbe.” Sai A’isha ta ce: “Ban bar aikin Hajji ba tun da na ji wannan daga Manzon Allah (SAW).”

334. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari daga Amru daga Abu Ma’abad bawan dan Abbas daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce, “Mace kada ta yi tafiya face tare da muharraminta (dan uwanta). Kuma kada wani namiji ya shiga ga mace face tana tare da wani muharraminta. Sai wani mutum ya ce, “Ya Manzon Allah! Hakika ina son fita zuwa yakin kaza da kaza amma matata, tana nufin zuwa Hajji,” sai (Annabi) ya ce, “Ka tafi tare da ita.”