Babi na Ashirin: Mai haramin da ya mutu a Arfa
Babi na Ashirin: Mai haramin da ya mutu a Arfa, amma Annabi (SAW) bai umarci a cika masa sauran aikin Hajjinsa ba323. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari daga Amru dan Dinar daga Sa’id dan Jubair daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: […]
Babi na Ashirin:
Mai haramin da ya mutu a Arfa, amma Annabi (SAW) bai umarci a cika masa sauran aikin Hajjinsa ba
323. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari daga Amru dan Dinar daga Sa’id dan Jubair daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Wata rana wani mutum yana tsaye tare da Annabi (SAW) a Arfa, sai ya fado daga kan taguwarsa ta kashe shi, (saboda karya masa wuya). Sai Annabi (SAW) ya ce, “Ku yi masa wanka da ruwa ku sanya magarya. Ku yi masa likkafani cikin tufafi biyu, ko ya ce, cikin tufafinsa. Amma kada ku sanya masa turare kuma kada ku rufe kansa. Domin hakika Allah zai tashe shi Ranar kiyama yana mai talbiyya (Labbaika lahumma labbaika).”
324. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Hammad ya ba mu labari daga Ayyub daga Sa’id dan Jubair daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Wata rana wani mutum na tsaye tare da Annabi (SAW) a Arfa, sai ya fado daga taguwarsa ta karya masa wuya. Annabi (SAW) ya ce, “Ku wanke shi da ruwa ku sanya magarya, ku yi masa likkafani a cikin tufafi biyu. Amma kada ku shafa masa turare kada ku rufe masa kansa. Hakika Allah zai ta she shi yana mai talbiyya.”
Babi na Ashirin da daya:
Sunnar mai Ihrami idan ya mutu
325. An karbo daga Yakub dan Ibrahim ya ce: “Abu Bishru ya ba mu labari daga Sa’id dan Jubair daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai wani mutum ya kasance tare da Annabi (SAW) sai taguwarsa ta kayar da shi ta karya masa wuya. Alhali yana mai Ihrami sai ya mutu, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku wanke shi da ruwa da magarya, kuma ku yi masa likkafani a cikin tufafi biyu. Kada ku shafa masa turare kada ku rufe masa kansa. Domin hakika za a ta she shi Ranar kiyama yana mai talbiyya.”
Babi na Ashirin da Biyu:
Yin Hajji tare da cika alwashi ga mamaci. Kuma namiji na iya Hajji ga mace
326. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Abu Awanata ya ba mu labari daga Abu Bishru daga Sa’id dan Jubair daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), cewa: “Wata daga kabilar Juhaina ta zo ga Annabi (SAW) ta ce: “Lallai mahaifiyata ta yi alwashi za ta yi Hajji amma ba ta yi Hajjin ba har ta mutu, shin zan iya yin mata Hajji? Ya ce, “Na’am, ki yi mata Hajjin, shin ba ki ganin da a ce akwai bashi a kan mahaifiyarki ke ce mai biya? To ki biya bashin Allah, domin Allah Shi Ya fi cancanta da a biya.”
Babi na Ashirin da uku:
Yin Hajji ga wanda bai iya zama kan abin hawa (kamar rakumi).
327. An karbo daga Abu Asim ya ce: “Daga dan Juraij daga dan Shihab daga Sulaiman daga dan Yassar daga dan Abbas daga Fadalu dan Abbas (Allah Ya yarda da su), cewa: Lallai wata mace ta zo ga Annabi (SAW) Hawwala Sanad. Ya ce, “Musa dan Isma’il ya ba mu labari ya ce, Abdul’aziz dan Abu Salma daga dan Shihab daga Sulaiman dan Yassar daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Wata mace daga kabilar Kas’ama ta zo ga (Annabi SAW) a shekarar Hajjin Ban-Kwana, sai ta ce: “Ya Manzon Allah! Lallai farillar Allah ta Hajji ta fada a kan mahaifina alhali ya tsufa tukuf bai iya zama kan doki (abin hawa), shin zai isar masa idan na yi masa Hajjin? Ya ce: “Na’am.”