Babi na Bakwai: Wanda ya ce, wa bawansa na bar shi ga Allah da niyyar ‘yantawa, kuma da shaidu bisa ‘yancin to ‘yantu:
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi Babi na Bakwai: Wanda ya ce, wa bawansa na bar shi ga Allah da niyyar ‘yantawa, kuma da shaidu bisa ‘yancin to ‘yantu:246. An karbo daga Muhammad dan Abdullahi dan Numair ya ce: “Daga Muhammad dan Bashir daga Isma’il daga kaisu daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da […]
Tare da Sheikh
Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi
Babi na Bakwai: Wanda ya ce, wa bawansa na bar shi ga Allah da niyyar ‘yantawa, kuma da shaidu bisa ‘yancin to ‘yantu:
246. An karbo daga Muhammad dan Abdullahi dan Numair ya ce: “Daga Muhammad dan Bashir daga Isma’il daga kaisu daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai shi (Abu Huraira) lokacin da ya nufin shiga Musulunci sai ya fita tare da bawansa. Sai kowane daga cikinsu biyu ya bace wa abokin (tafiyarsa). Ana nan haka sai bawan ya iso alhali Abu Huraira na zaune tare da Annabi (SAW), sai Annabi (SAW) ya ce: Ya Abu Huraira! Wannan bawanka ne, ga shi ya zo maka. Sai (Abu Huraira) ya ce: “Amma lallai ni, ina shaida maka cewa, lallai shi ’yantacce ne (na ’yanta shi).” Ya ce, “Lokaci ne da Abu Huraira ke rera wannan wake: Kaicon tsawon dare da wahalarsa. Duk da haka ita ce ta fitar da mu daga garin kafirci.”
247. An karbo daga Ubaidullahi dan Sa’id ya ce: “Abu Usamatu ya ba mu labari ya ce, Isma’il ya ba mu labari daga kaisu daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Lokacin da na gabata ga Annabi (SAW) na ce: A cikin hanyar tafiyata: “Kaicon dare mai tsawo da wahalarwa. Bisa fitar da mu daga garin kafirci.” Ya ce, “Sai bawana ya gudu daga gare a cikin hanyar,” ya ce, lokacin da na gabata (isa) ga Annabi (SAW) na yi masa mubaya’a ina tare da shi cikin wannan hali, sai bawan nan nawa ya bullo, sai Manzon Allah (SAW) ya ce, mini: “Ya Abu Huraira! Wannan bawanka ne ga shi ya zo.” Sai na ce, “Na ’yanta shi domin Allah,” Abu Abdullahi ya ce: “Abu Kuraibu bai ambaci haka ba daga Abu Usamatu wato, ’yantacce.”
248. An karbo daga Shihab dan Abbad ya ce: “Ibrahim dan Humaid ya ba mu labari daga Isma’il daga kaisu ya ce: “Lokacin da Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya fita shi da bawansa suna neman shiga Musulunci sai suka bace wa juna da kamar abin da ya gabata. Sai (Abu Huraira) ya ce: “Amma lallai ni, ina shaida maka na bar shi domin Allah.”
Babi na Takwas: Bai wa uwar ’ya’ya. Abu Huraira ya ce, daga Annabi (SAW) cewa: “Na daga alamar tashin kiyama baiwa ta haifi shugabanta.”:
249. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Urwatu dan Zubair daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Lallai Utbatu dan Abu Wakkas ya yi alkawarin (kyautar da) ga dan uwansa Sa’ad dan Abu Wakkas da ya karba masa dan baiwar Zama’atu. Utbatu ya ce, “Lallai shi yaron dana ne, lokacin da Manzon Allah (SAW) ya iso azamanin cin Makka da yaki. Sai Sa’ad ya karbe dan baiwar nan daga Zama’atu ya tafi da shi wajen Manzon Allah (SAW), sai Abdu dan Zama’a ya bi shi, Sa’ad ya ce, ya Manzon Allah! Wannan dan danuwana ne wanda ya yi mini alkawari da shi cewa dansa. Sai Abdu dan Zama’atu ya ce, “Ya Manzon Allah! Wannan dan uwana ne dan baiwar Zama’atu wanda aka haifa bisa shimfidarsa.” Lokacin da Manzon Allah (SAW) ya yi dubi zuwa ga dan baiwar Zama’atu sai ya gan shi babu wanda ya fi kama da shin cikin mutane face shi (Zama’atu). Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Shi naka ne, Ya Abdu dan Zama’atu saboda an haife shi ne bisa shimfidar Babansa.” Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya Saudatu ’yar Zam’atu ki tsare kanki daga gare shi, saboda abin da ya gani na kamanninsa da Utbah domin Saudatu ta kasance matar Annabi (SAW).”
Babi na Tara: Hukuncin sayar da bawan da aka rubuta ’yancinsa ta sanya masa ajalin haka bayan mutuwar shugabansa:
250. An karbo daga Adam dan Abu Iyas ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Amru dan Dinar ya ba mu labari ya ce: “Na ji Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Wani mutum daga cikinmu ya taba ’yanta wani bawansa ta hanyar ’yanci bayan mutuwar shugabansa. Sai Annabi (SAW) ya kira shi (bawan) ya sayar da shi.” Jabir ya ce: “Bawan ya mutu ne a farkon shekarar.”