Babi na Biyar:

Mai Ihrami ba ya nuna abin farauta saboda wanda ba ya da Ihrami ya farauce shi 299. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Abu Awanata ya ba mu labari ya ce, Usman dan Mauhib ya ba mu labari, ya ce: Abdullahi dan Abu kattada ya ba mu labari, cewa: Lallai Babansa ya ba […]

Babi na Biyar:
Babi na Biyar:

Mai Ihrami ba ya nuna abin farauta saboda wanda ba ya da Ihrami ya farauce shi

299. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Abu Awanata ya ba mu labari ya ce, Usman dan Mauhib ya ba mu labari, ya ce: Abdullahi dan Abu kattada ya ba mu labari, cewa: Lallai Babansa ya ba shi labari cewa, Lallai Manzon Allah (SAW) ya fita zuwa Hajji, sai wasu jama’a suka fita tare da shi amma wasu daga cikinsu sun saba hanyar tafiya daga cikinsu akwai Abu kattada, sai ya ce: “Ku bi gabar kogin nan, har sai mun hadu, sai suka kama bin gabar kogin da suka juya sai suka yi Ihrami dukkansu face Abu kattada bai yi Ihrami ba. Ana cikin haka suna tafiya sai suka hangi jakunan dawa (daji). Abu kattada ya kai hari ga jakunan ya soke jaka daya daga cikinsu. Suka sauka suka ci daga namanta, wasu suka ce, “Shin za mu ci alhali muna da Ihrami? Sai muka dauki sauran naman jakar. Lokacin da muka je ga Manzon Allah (SAW) muka ce: “Ya Manzon Allah! Lallai mun kasance mun yi Ihrami amma Abu kattada bai yi Ihrami ba, sai muka hangi jakunan dawa. Sai Abu kattada ya kai mata hari ya soke wata jaka (da mashi) daga cikinsu, muka sauka muka ci daga namanta. Sa’an nan muka ce, “Shin za mu ci naman farauta alhali muna masu Ihrami? Sai muka dauko abin da ya saura daga namanta. (Annabi SAW) ya ce, “Daga cikinku akwai wanda ya umarce shi da ya kai mata hari, ko wani ya nuna masa ita? Su ka ce, “A’a,” ya ce, “Ku ci abin da ya saura daga namanta.”

Babi na Shida:
Idan aka yi wa mai Harami kyautar jakin dawa rayayye kada ya karba

300. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga dan Shihab daga Ubaidullahi dan Abdullahi dan Utbah dan Mas’ud daga Abdullahi dan Abbas daga Sa’ab dan Jassama Allaisiyyu cewa: Lallai shi ya yi wa Manzon Allah (SAW) kyautar jakin dawa lokacin shi (Annabi SAW) na Abwa’u ko Waddan sai ya mayar masa. Lokacin da (Annabi) ya ga abin da ke fuskarsa (Jassama na baki ciki) sai ya ce: “Lallai mu, ba mu mayar maka da shi (don haramcinsa) ba, face saboda hakika muna cikin Ihrami.”

 Babi na Bakwai:
Abin da aka halatta wa mai harami kashewa daga dabbobi

301. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Dabbobi biyar babu laifi ga mai harami idan ya kashe su.” Daga Abdullahi dan Dinar ya ce, daga Abdullahi dan Umar cewa: Lallai Manzon Allah (SAW) ya fadi haka.”

302. An karbo daga Musaddad ya ce: “Abu Awanata ya ba mu labari daga Zaid dan Jubair ya ce, “Na ji dan Umar (Allah Ya yarda da su) yana cewa: “daya daga cikin matan Annabi (SAW) ta ba ni labari daga Annabi (SAW) ya ce: “Mai harami zai iya kashe wasu dabbobi biyar.”

303. An karbo daga Asbagh dan Farj ya ce: “Abdullahi dan Wuhaib ya ba ni labari daga Yunus daga dan Shihab daga Salim ya ce: “Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce, “Hafsatu ta ce, “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Dabbobi biyar babu laifi mai harami ya kashe su: Hankaka da shirwa da bera da kunama da mahaukaci kare.”