BABI NA BIYAR:(1)

BABI NA BIYAR:Wanda ya tsinci itace (ko katako) ko wata bulala ko makamancin haka a cikin kogi yaya zai yi. Laisu ya ce, “Ja’afar dan Rabi’ata ya ba ni labari daga Abdurrahman dan Hurmuz daga Abu Huraira (Allah ya yarda da shi), daga Manzon Allah (SAW) cewa: “Lallai shi ya ambaci wani Bani Is’rail da […]

BABI NA BIYAR:(1)
BABI NA BIYAR:(1)

BABI NA BIYAR:
Wanda ya tsinci itace (ko katako) ko wata bulala ko makamancin haka a cikin kogi yaya zai yi. Laisu ya ce, “Ja’afar dan Rabi’ata ya ba ni labari daga Abdurrahman dan Hurmuz daga Abu Huraira (Allah ya yarda da shi), daga Manzon Allah (SAW) cewa: “Lallai shi ya ambaci wani Bani Is’rail da ya biya bashi ta cikin rakakken itace; kamar yadda ya bata sai ya kora Hadisin bisa cewa: Wanda ya ke bin bashi sai ya rika duban gabar teku ko mahayin ya komo masa da dukiyarsa sai ya iske wani itace ya dauke shi zuwa ga iyalansa a matsayin itacen wuta. Lokacin da ya faskare itacen sai ya iske kudin da wata takarda tare da ita. (wadda take shaidar dukiyarsa ce da ke bi bashi).”

BABI NA SHIDA:
Idan mutum ya tsinci dabino a kan hanya:
151. An karbo daga Muhammad dan Yusuf ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Mansur daga dalhat daga Anas (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Wata rana Annabi (SAW) ya shude da wani dabino a cikin hanya sai ya ce: “Ba domin ina jin tsoron kada ta kasance ko ta sadaka ce ba da na ci.”
152. An karbo daga Sufiyan ya ce: “Mansur ya ba ba ni labari ya ce, Za’idat ya ba ni labari daga Mansur daga dalhat ya ce, “Anas ya ba mu labari ya ce, Muhammad dan Mukatil ya ba mu labari ya ce, Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Hammam dan Munabbih daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Wata rana nakan komo zuwa ga iyalina sai na iske dabino ta fadi bisa kan shimfidata sai in dauke ta don ci sa’an nan sai in ji tsoron kada ta kasance ta sadaka ce sai in jefar da ita.” (Wannan ya nuna Annabi bai cin sadaka ne).
 
BABI NA BAKWAI:
Yadda ake sanar da abin tsuntuwar mutane a garin Makka. dawus ya ce, daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), daga Annabi (SAW) ya ce: “Ba a daukar tsuntuwarta (Makka) face ga wanda zai sanar da ita.” Khalid ya ce, daga Ikramata daga dan Abbas daga Annabi (SAW) ya ce: “Ba a daukar abin tsuntuwarta (Makka) face ga wanda zai sanar.” Ahmad dan Sa’id ya ce, “Rauhu ya ba mu labari ya ce, Zakariya ya ba mu labari ya ce, Amru dan Dinar ya ba mu labari daga Ikramata daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ba a cire kayarta wanda bai cutarwa. Kuma ba a korar abin farautarta, kuma abin tsuntuwarta ba ya halatta face ga mai sanarwa. Kuma ba a cire makiyayanta.” Sai Abbas ya ce, “Ya Manzon Allah! Sai dai ban da ciyawar tsaure.” Sai (Annabi) ya ce: “To ban da ciyawar tsaure.”