Babi na Biyu: bataccen rakumi da hukunci mai tsuntuwa:

148. An karbo daga Amru dan Abbas ya ce: “Abdurrahman ya ba mu labari ya ce, Sufiyan ya ba mu labari daga Rabi’ata ya ce, Yazid bawan Munba’is ya ba ni labari daga Zaid dan Khalid Juhani (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Wani Balaraben kauye ya zo ga Annabi (SAW) ya tambaye shi […]

Babi na Biyu: bataccen rakumi da hukunci mai tsuntuwa:
Babi na Biyu: bataccen rakumi da hukunci mai tsuntuwa:

148. An karbo daga Amru dan Abbas ya ce: “Abdurrahman ya ba mu labari ya ce, Sufiyan ya ba mu labari daga Rabi’ata ya ce, Yazid bawan Munba’is ya ba ni labari daga Zaid dan Khalid Juhani (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Wani Balaraben kauye ya zo ga Annabi (SAW) ya tambaye shi game da abin da ya tsinta. Sai (Annabi SAW) ya ce, “Ka sanar da ita, shekara daya, sa’an nan ka sanar da abin da ke cikin jakar da kamannin jakar. Idan mai ita ya zo ya ba ka labari game da ita, to shi ke nan ka ba shi ita. Idan ba haka ba sai ka yi amfani da ita.” Sai ya ce, “Ya Manzon Allah! batacciyar tunkiya fa? Ya ce, “Naka ne ko na dan uwanka, ko na kerkeci.” Ya ce, “bataccen rakumi fa? Sai fuskar Manzon Allah (SAW) ta yi ja. Ya ce, “Me ya hada ka da shi? Tana da takalmanta da abin shanta, tana tanadin ruwa tana cin itatuwa.”
Babi na Uku: batacciyar tunkiya:
149. An karbo daga Isma’il dan Abdullahi ya ce: “Sulaiman dan Bilal ya ba mu labari daga Yahya daga Yazid bawan Munba’is cewa, lallai shi ya ji Zaid dan Khalid (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “An tambayi Annabi (SAW) game da tsuntuwa, sai (mutumin) ya riya cewa: (Annabi) ya ce, “Ka sanar da abin da ke cikin kunshin (jaka) da yadda kunshin kaya yake. Sa’an nan ka sanar da ita shekara daya.” Yazid yana cewa: “Idan babu wanda ya ce, nasa ne, wanda ya tsinta yana iya amfani da ita, ta kasance masa kamar ajiya ce.” Yahya ya ce, “Wannan ne ban sani ba shin ko na cikin Hadisin ne ko kuwa a’a wani abu daga gare shi (Yazid)? Sa’an nan (mutumin ya ce da Annabi): “Me ka gani game da batacciyar tunkiya?” Annabi (SAW) ya ce, “Ka kama ta, domin taka ce, ko ta dan uwanka, ko ta kerkeci.” Yazid ya ce, “Ita ma za a sanar,” sa’an nan (mai tambaya) ya ce: “To me ka gani game da bataccen rakumi? Ya ce: “Ka bar shi domin lallai shi, yana tare da takalmansa da abin shansa yana tanadin ruwa kuma yana cin itatuwa har mai shi ya iske shi.”
Babi na Hudu: Idan ba a samu mai kayan tsuntuwa ba a bayan shekara daya, to yana ga wanda ya tsinta ya yi amfani da shi:
150. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Rabi’ata dan Abu Abdurrahman daga Yazid bawan Munba’is daga Zaid dan Khalid (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Wani mutum ya zo ga Manzon Allah (SAW) ya tambaye shi game da tsintuwa sai (Annabi) ya ce: “Ka sanar da (shelar) abin da ke cikin kunshin kayan. Da yadda jakar take, sa’an nan ka sanar da ita shekara daya, idan mai ita ya zo ka ba shi, idan ba haka ba, to ka yi sha’aninka da ita.” Sai (mai tambaya) ya ce: “batacciyar tunkiya fa? Ya ce, “Taka ce, ko ta dan uwanka ko kerkeci.” Ya ce, “bataccen rakumi fa? Ya ce, “Me ya hada ka da shi? Yana tare da abin shansa da kofatonsa yana tanadin ruwa yana cin itatuwa har mai shi ya hadu da shi.”