Babi na dari da Bakwai: Laifin wanda ya sayar da dan Adam (wanda ba bawa ba):
669. An karbo daga Bishiru dan Marhum ya ce: “Yahya dan Sulaim ya ba mu labari daga Isma’ilu dan Umayyata daga Sa’ad dan Abu Sa’id ya ce: ‘Daga Abu Huraiara (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Allah Ya ce: Mutum uku Ni ne Mai husuma da su Ranar kiyama: (1) Mutumin […]
669. An karbo daga Bishiru dan Marhum ya ce: “Yahya dan Sulaim ya ba mu labari daga Isma’ilu dan Umayyata daga Sa’ad dan Abu Sa’id ya ce: ‘Daga Abu Huraiara (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Allah Ya ce: Mutum uku Ni ne Mai husuma da su Ranar kiyama: (1) Mutumin da aka ba shi alkawari da ni (Allah) ya yi yaudara. (2) Mutumin da ya sayar da dan Adam (mai ’yanci) ya ci kudinsa. (3) Mutumin da ya yi jinga da wani mutum ya gama masa aiki bai biya shi ladansa (jingansa) ba.”
Babi na dari da Takwas: Umarnin Annabi (SAW) ga Yahudawa da su sayar da kasarsu lokacin da ya kore su. Daga cikin wadanda suka karbo haka akwai Makburi daga Abu Huraira:
Babi na dari da Tara:
Cinikin bawa da cinikin dabba da dabba bisa jinkiri.
dan Umar ya sayi abin hawa daya da rakuma hudu wadanda ya yi alkawarin biyan mai shi a Rabza. danA bbas ya ce, “Lallai wani rakumi guda yakan kasance ya fi wasu rakuma biyu.” Rafi’u dan Khadija ya sayi wani rakumi bisa rakumi biyu, ya bayar da daya ya ce, zan zo maka da dayan gobe ba tare da bata lokaci ba idan Allah Ya so.” dan Musayyib ya ce, “Babu riba a cikin dabbobi, rakumi daya bisa rakumi biyu, akuya daya bisa akuya biyu zuwa wani lokaci.” dan Sirin ya ce, “Babu laifi cikin rakumi daya bisa rakumi biyu nisa (jinkiri).”:
670. An karbo daga Sulaiman dan Harbu ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari daga Sabit daga Anas (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Ya kasance daga cikin fursunonin yakin da aka yi da (Annabi SAW) da wata mace mai suna: Safiya, sai ta kasance a cikin rabon Dihyatul Kalbi, sa’an nan daga baya ta kasance zuwa ga Annabi (SAW).”
671. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, dan Muhairizin yana cewa: “Lallai Abu Sa’idul Khudri (Allah Ya yarda da shi) ya ba shi labari cewa: “Lallai shi ya ce, wata rana yana zaune a wurin Annabi (SAW) ya ce: “Ya Manzon Allah! Lallai mu mukan samu kamammun yaki (fursunoni), kuma muna son kuyangi, to, me ka gani idan muka rika tarawa da su amma ba mu barin maniyyi cikin farjinsu saboda tsoron kada su haihu? (Annabi) Ya Ce: “Shin ku kuke aikata haka? Kada ku aikata haka. Babu wata halitta da Allah Ya wajabta za ta fito face sai ta fita.”
Babi na dari da Goma: Cinikin wanda aka ’yanta bayan mutuwa:
672. An karbo daga dan Numair ya ce: “Waki’u ya ba mu labari ya ce, Isma’il ya ba mu labari daga Salmata dan Kuhail daga Adda’u daga Jabir (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya sayar da mudabbari (wanda aka ’yanta bayan mutuwar shugabansa) saboda wata bukata.”
673. An karbo daga kutaiba ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Amru ya ce, ya ji Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya sayar da shi (Mudabbari) saboda wata bukata.”