BABI NA GOMA
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Babu saduwa da mace, (a Hajji) (2:197).”294. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari daga Mansur daga Abi Hazim daga Abi Huraira, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Wanda ya yi Hajji a […]
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus
Almashgool, Bauchi
Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Babu saduwa da mace, (a Hajji) (2:197).”
294. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari daga Mansur daga Abi Hazim daga Abi Huraira, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Wanda ya yi Hajji a wannan daki, bai sadu da mace ba, kuma bai yi fasikanci ba, zai koma gida ba shi da zunubi, kamar yanda uwarsa ta haife shi.”
BABI NA GOMA SHA dAYA:-
Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Babu fasikanci babu jayayya a cikin Hajji..(2:197).”
295. An karbo daga Muhammad dan Yusuf ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari, daga Mansur daga Abi Hazim daga Abi Huraira, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Annabi (S.A.W) ya ce, “Wanda ya yi Hajjin wannan daki, bai sadu da mace ba, kuma bai yi fasikanci ba, zai koma gida babu zunubi tare da shi, kamar yinin da uwarsa ta haife shi.”
Da Sunan Allah, Mai Rahma, Mai Jinkai.
BABI NA FARKO:-
Sakamakon farauta a cikin aikin Hajji ko Umra da makamancinsa. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Kada ku kashe abin farauta alhali kuna a cikin Harami. Wanda ya kashe shi (farauta) daga cikinku da ganganci to, sakamakonsa misalin abin da ya kashe daga dabbar gida….har zuwa fadarSa cewa: ‘Ku ji tsoron Allah, Wanda zuwa gare Shi ake tara ku (5:95-96).”
BABI NA BIYU:-
Idan wanda ba shi da Ihrami ya yi farauta ya ba da naman ga wanda ke cikin Harami, shin zai ci shi (naman)? dan Abbas da Anas ba su ganin laifi ga wanda yake da Ihrami idan ya yanka dabbar da ba na farauta ba, kamar rakumi da tinkiya da saniya da kaza da doki.”
296. An karbo daga Mu’adhu dan Fudalah ya ce: “Hisham ya ba mu labari, daga Yahya daga Abdullahi dan Abi katada ya ce; “Mun tafi tare da Babana a shekarar Hudaibiyya, abokansa suka yi Ihrami, amma shi bai yi Ihrami ba. Sai aka ba Annabi (S.A.W) labari cewa: Lallai makiya za su yake shi, sai Annabi (S.A.W) ya ci gaba, ana cikin haka Babana na tare da abokansa, sai ya ji suna dariya sashensu da sashe. Sai (Babana) ya ce, “Na duba (waiwaya) sai ga jakin dawa, sai na kai masa hari na soke shi, na kama shi. Na nemi abokaina su taimake ni, sai suka ki taimakona. Sai muka ci daga namansa, daga nan muka ji tsoron kada a katse mu (daga Annabi), sai na rika neman Annabi (S.A.W), sai in zaburar da abin hawata da gudu, sai in tafi da saukaka, sai na hadu da wani mutum daga kabilar Ghifar, a cikin duhun dare, na ce: “Ina ka bar Annabi (S.A.W)?” Ya ce, “Na bar shi a Ta’ahun, yana nufin isa Sukyah don ya huta a can”. Sai (muka isa gare shi) na ce, “Ya Manzon Allah! Lallai mutanenka na karanta (yi) maka sallama da rahamar Allah. Amma kuma lallai su, sun ji tsoron kada a katse tsakaninsu da kai, ko za ka saurara musu?” Sai na ce, “Ya Manzon Allah! Na yi farautar jakin dawa, kuma akwai saura tare da ni.” Sai (Annabi) ya ce musu: “Ku ci”, alhali suna cikin Ihrami.”