Babi na Goma: Hukuncin cinikin ’yancin bawa da kyautarsa.

251. An karbo daga Abul Walid ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Abdullahi dan Dinar ya ba ni labari ya ce: “Na ji dan Umar (Allah Ya yarda da su), yana cewa: “Annabi (SAW) ya hana game da cinikin ’yancin bawa ko kyautar da shi.”252. An karbo daga Usman dan Abu Shaibah […]

Babi na Goma: Hukuncin cinikin ’yancin bawa da kyautarsa.
Babi na Goma: Hukuncin cinikin ’yancin bawa da kyautarsa.

251. An karbo daga Abul Walid ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Abdullahi dan Dinar ya ba ni labari ya ce: “Na ji dan Umar (Allah Ya yarda da su), yana cewa: “Annabi (SAW) ya hana game da cinikin ’yancin bawa ko kyautar da shi.”
252. An karbo daga Usman dan Abu Shaibah ya ce: “Jarir ya ba mu labari daga Mansur daga Ibrahim daga Aswad daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Na sayi Barirah sai shugabanninta suka shardanta waliccinta na gare su. Sai na ambaci haka ga Annabi (SAW) sai ya ce: “Ki ’yantata amma lallai ’yanci (walicci) na ga wanda ya biya azurfa kuma ’yanta ta. Annabi (SAW) ya kira ta, ya ba ta zabin daga mijinta sai ta ce: “Da a ce, ya ba ni dukiya mai yawa kamar kaza da kaza da ban tabbata gare shi ba, sai ta zabi kanta.”
Babi na Goma Sha daya:
Idan aka kama dan uwan mutum a yaki ko aka kama baffansa shin zai iya fansarsa ko da ya kasance arne ne (mushiriki). Anas ya ce: “Abbas ya ce ga Annabi (SAW) cewa: “Na fanshi kaina, kuma ni na fanshi Akil, kuma Aliyu ya kasance na da kaso (rabo) cikin wannan ganima wadda ya samu daga dan uwansa Akil da baffansa Abbas.
253. An karbo daga Isma’il dan Abdullahi ya ce: “Isma’il dan Ibrahim dan Ukbatu ya ba mu labari daga Musa dan Ukbatu daga dan Shihab ya ce: “Anas (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai wadansu mutane daga cikin mutanen Madina da suka nemi izinin Manzon Allah (SAW) sai suka ce: “Ka yi mana izini mu bar (yafe) wa dan ’yar uwanmu Abbas fansarsa.” Sai (Annabi) ya ce: “Kada ku yafe masa ko da dirhami daya.”

Babi na Goma Sha Biyu: Hukuncin wanda ya rika ’yanta bayi mushirikai.
254. An karbo daga Ubaidu dan Isma’il ya ce: “Abu Usamatu ya ba mu labari daga Hisham ya ce, hakika babana Hakim dan Hizam (Allah Ya yarda da shi) ya taba ’yanta bayi dari a Jahiliyya kuma ya taba yanka rakuma dari. Lokacin da ya musulunta sai da ya taba yanka rakuma dari, kuma ya ’yanta bayi dari. Ya ce, “Na tambayi Manzon Allah (SAW), na ce, “Ya Manzon Allah! Shin ka ga ni game da abubuwan da na kasance in aikatawa a cikin Jahiliyya, wadanda nake nufin neman lada da su (shin ina da sakamako cikin Musulunci). Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ka musulunta bisa ga abin da ya gabata gare ka na alheri (wato yana da sakamako).”

Babi na Goma Sha Uku:
Wanda ya mallaki wani bawa cikin Larabawa sai ya yi kyauta da shi ko ya sayar, ko ya sadu da ita (baiwa) ko ya fanshi bawan ko ya kama bayi daga danginsa. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Allah Ya buga misali kamar bawan da aka mallaka wanda bai da iko bisa komai da (misalin) wanda Muka azurta da arziki mai kyawo daga wurinMu alhali shi na ciyarwa boye da bayyane. Shin za su zamo tamkar daya (amsa a’a). Ka ce, Godiya ta tabbata ga Allah, amma dai mafi yawan mutane ba su da sani (16:75).”