Babi na Goma Sha Bakwai: Sanya haraji ga bayi ta wajen shugabanninsu da bayanin sanya haraji ga kuyangi:

Babi na Goma Sha Bakwai: Sanya haraji ga bayi ta wajen shugabanninsu da bayanin sanya haraji ga kuyangi:17. An karbo daga Muhammad dan Yusuf ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Humaid dawil daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Abu dayyib ya yi wa Annabi (SAW) kaho, sai ya […]

Babi na Goma Sha Bakwai: Sanya haraji ga bayi ta wajen shugabanninsu da bayanin sanya haraji ga kuyangi:
Babi na Goma Sha Bakwai: Sanya haraji ga bayi ta wajen shugabanninsu da bayanin sanya haraji ga kuyangi:

Babi na Goma Sha Bakwai: Sanya haraji ga bayi ta wajen shugabanninsu da bayanin sanya haraji ga kuyangi:
17. An karbo daga Muhammad dan Yusuf ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Humaid dawil daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Abu dayyib ya yi wa Annabi (SAW) kaho, sai ya umarta da a ba shi awon sa’i daya ko sa’i biyu na abinci. Kuma ya yi wa shugabansa magana da ya saukaka masa haraji.”

Babi na Goma Sha Takwas: Ladar mai yin kaho:
18. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Wuhaib ya ba mu labari ya ce, dan dawus ya ba mu labari daga Babansa daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya yi kaho kuma ya biya mai kahon ladarsa.”
19. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yazid dan Zurai’u ya ba mu labari daga Khalid daga Ikramata daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya yi kaho kuma ya biya mai kahon ladarsa da dai ya san haramcinsa da bai biya shi ba.”
20. An karbo daga Abu Nu’aim ya ce: “Mis’ar ya ba mu labari daga Amru dan Amir ya ce, na ji Anas (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Annabi (SAW) ya kasance yana yin kaho, kuma bai kasance yana zaluntar wani (mai sana’ar yin kaho) ba kan ladarsa.”

Babi na Goma Sha Tara: Wanda ya yi magana ga shugaban bawa don ya saukaka masa haraji:
21. An karbo daga Adam ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Humaid dawili daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya kira wani saurayi wanda yake yin kaho, ya yi masa kaho, ya umarta da a biya shi sa’i daya ko sa’i biyu na abinci ko ya ce, muddi daya ko muddi biyu. Sai (Annabi) ya yi magana a kansa don a saukaka masa harajinsa (kudin fansa).”

Babi na Ashirin:
Hukuncin amfani da dukiyar zina da bayanin kuyangi (bayi mata). Ibrahim ya hana cin kudin baiwa mai kukan mutuwa da cin kudin baiwa mawakiya. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Kada ku tilasta kuyanginku (bayinku mata) bisa ga yin zina, matukar sun nemi tsare kansu (ta hanyar aure) domin ku nemi jin dadin duniya, wadda aka tilasta su (daga kuyangi). Hakika Allah bayan tilasta su Mai gafara ne Mai jinkai (k:24:33).”Mujahid ya ce, “Ma’anar ’yan matanku, wato kuyanginku.”
22. An karbo daga kutaiba dan Sa’id ya ce: “Malik ya ba mu labari daga dan Shihab daga Abubakar dan Abdurrahman dan Haris dan Hisham daga Abu Mas’ud mutumin Madina (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya hana game da cin kudin kare, ya hana cin kudin zina da shaci-fadi (kare-rayin) boka.”
23. An karbo daga Muslim dan Ibrahim ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Muhammad dan Juhadat daga Abu Hazim daga Abu Huraira (Allah Ya yarda) da shi ya ce: “Annabi (SAW) ya hana game da amfani da kudin zina ta hanyar sanya kuyangi zina.”

Babi na Ashirin da daya: Karbar kudin maniyyin rakumi domin barbarar taguwa:
24. An karbo daga Musaddad ya ce: “Abdulwaris ya ba mu labari da Isma’il dan Ibrahim daga Aliyu dan Alhakam daga Nafi’u daga Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya hana karbar kudin maniyyin rakumi saboda ya yi barbarar taguwa (macen rakuma.)”

Babi na Ashirin da Biyu:
Idan mutum biyu suka kulla jingar (hayar) wata kasa sai dayansu ya mutu. dan Sirin ya ce, “Ba ya yiwuwa magadar mamaci su fitar da shi (abokin jingar) face har sai ajalin ya cika.” Alhakamu da Alhasan da Iyas dan Mu’awiyyata sun ce, “Hayar za ta ci gaba har zuwa ajalinta.” dan Umar ya ce: “Annabi (SAW) ya bayar da (hayar) rabin amfanin gonakin Khaibara, haka ya kasance a zamanin Annabi (SAW) da Abubakar da rabin lokacin halifancin Umar. Abubakar bai nemi sabunta jingar hayar ba bayan da Allah Ya karbi ran Annabi (SAW).”