Babi na Goma Sha Biyar: Wanda ya daidaita rabon tumaki goma bisa ga rakumi daya:

24. An karbo daga Muhammad ya ce: “Waki’u ya ba mu labari daga Sufiyan daga Babansa daga Abayat dan Rifa’a daga kakansa Rafi’u dan Khadeej (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Mun kasance tare da Annabi (SAW) a Zul-Hulaifa mun komo daga Tihama sai muka samu ganimar tumaki da rakuma. Sai mutane suka yi […]

Babi na Goma Sha Biyar: Wanda ya daidaita rabon tumaki goma bisa ga rakumi daya:
Babi na Goma Sha Biyar: Wanda ya daidaita rabon tumaki goma bisa ga rakumi daya:

24. An karbo daga Muhammad ya ce: “Waki’u ya ba mu labari daga Sufiyan daga Babansa daga Abayat dan Rifa’a daga kakansa Rafi’u dan Khadeej (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Mun kasance tare da Annabi (SAW) a Zul-Hulaifa mun komo daga Tihama sai muka samu ganimar tumaki da rakuma. Sai mutane suka yi gaggawar dafuwa, suka dora tukwane, sai Manzon Allah (SAW) ya iso, ya yi umarni aka kashe wutarta. Sa’an nan ya yi rabo bisa daidaiton tumaki goma bisa ga rakumi daya. Ana cikin haka sai wani rakumi daga cikinsu ya kwace da gudu babu komai cikin jama’a face dawaki kadan, sai wani mutum ya bi shi ya harbe shi da kibiya wajen kama shi. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Dabbobi irin wadannan suna da halaye marasa kyau kamar namun dawa (daji) duk sa’adda suka yi irin wadannan halaye ku aikata da su kamar haka (wato ku harbe su).” Ya ce, “Sai kakana ya ce, “Ya Manzon Allah! Muna kauna tare da tsoron haduwa da abokan gaba gobe, kuma ba mu da makamin yanka, shin za mu iya yanka da iwa ko kyauro? Sai ya ce, “To shi ke nan, duk dai abin da yake zubar da jini kuma an ambaci sunan Allah kansa, to ku ci shi, amma ban da hakori da akaifa (farce). Kuma zan ba ku labari game da haka, amma kun ga hakori kashi ne, akaifa kuma wukar Habashawa ce.”

 

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.
Littafin Bayanin Jingina a cikin halin zaman gida.

Babi na Farko: Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Idan kun kasance kuna matafiya ba ku samu mai rubutu ba, sai ya zama jingina abar karba… (k:2:283):
225. An karbo daga Muslim dan Ibrahim ya ce: “Hisham ya ba mu labari ya ce, kattada ya ba mu labari daga Anas (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Hakika Annabi (SAW) ya jinginar da taguwarsa na sulke bisa ga sha’iri. Wata rana na tafi da waina na sha’iri da daskararen mai ga Manzon Allah (SAW) sai na ji shi yana cewa: “Babu abin da ya kwana ga Ali-Muhammad na hatsi face sa’i daya, alhali lallai shi yana da dakuna (mata) tara.”

Babi na Biyu: Wanda ya jinginar da taguwarsa ta sulken yaki:
226. An karbo daga Musaddad ya ce: “Abdulwahid ya ba mu labari ya ce, A’amashi ya ba mu labari ya ce, mun yi hirar jingina hukuncin karbar kayan sautu (fatauci). Sai Ibrahim ya ce, “Aswad ya ba mu labari daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Hakika Annabi (SAW) ya sayi abinci bashi zuwa ga wani ajali daga wajen wani Bayahude sai ya jinginar masa da sulkensa.”

Babi na Uku: Jinginar makami:
227. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Amru ya ce, “Na ji Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su) yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Wane ne zai yi mini maganin Ka’ab dan Ashraf! Domin lallai shi ya cutar da Allah da ManzonSa (SAW), sai Muhammad dan Salmat ya ce, “Ni zan aikata,” sai ya je masa ya ce: “Muna son ka yi mana salafin (ka ba mu) wasaki daya ko wasaki biyu, sai ya ce: “Ku yi mana jinginar matanku,” sai suka ce, “Kamar yaya za mu yi maka jinginar matanmu alhali kai ne mafi kyawun Larabawa? Sai ku yi mini jinginar yaranku,” suka ce, “Kamar yaya za mu yi maka jinginar yaranmu, idan an yi fada da dayansu sai a rika ce masa, wanda aka yi jinginarsa bisa wasaki daya ko wasaki biyu? Wannan ai tsaraitawa (tonon asiri) ne gare mu, amma dai mu za mu yi maka jinginar makaminmu.” Sai Sufiyan ya ce, “Yana nufin makamansu na yaki, sai ya yi masa wa’adi zai je masa, sai ya kashe shi. Sa’an nan ya tafi ga Annabi (SAW) ya ba shi labarin (abin da ya faru tsakaninsu).”