Babi na Goma Sha Biyu:

Hukuncin wanda ya yi jinga da dan kwadago sai shi dan kwadagon ya bar kudin jingar bai amsa ba, sai wanda ya ba shi jinga ya yi aiki (kasuwanci) cikin shi (kudin jingar) har ya karu. Ko kuma wanda ya yi aiki (kasuwanci) cikin dukiyar wani ya samu kari (riba): 12. An karbo daga Abul […]

Babi na Goma Sha Biyu:
Babi na Goma Sha Biyu:

Hukuncin wanda ya yi jinga da dan kwadago sai shi dan kwadagon ya bar kudin jingar bai amsa ba, sai wanda ya ba shi jinga ya yi aiki (kasuwanci) cikin shi (kudin jingar) har ya karu. Ko kuma wanda ya yi aiki (kasuwanci) cikin dukiyar wani ya samu kari (riba):

12. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, “Salim dan Abdullahi ya ba mu labari, cewa: “Lallai Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Wasu mutum uku daga wadanda suke gabaninku, wata rana sun fita zuwa wata tafiya sai dare ya yi musu, suka shiga wani kogo domin su kwana suka shige shi, sai wani falale na dutse ya fado daga bisan duste ya rufe su cikin kogon. Sai suka ce, “Babu abin da zai fitar da (tserarar da) ku face ku roki Allah da mafi kyawn ayyukanku. Sai wani mutum daya daga cikinsu ya ce, “Ya Allah! Ya kasance mini ina da iyaye biyu tsofaffi tukuf kuma na kasance ban gabatar da komai gabaninsu ga iyalaina ko dukiyata. Wata rana sai neman abin da za mu ci ya shagaltar da ni ban komo gare su da wuri ba, face har sun yi barci, sai na yi musu tattalin madara domin in shayar da su, sai na iske su suna barci. Sai na ji tsoron kada in farkar da su kuma ban son in fara da iyalaina ko da dukiyata. Sai na zauna da gorar bisa hannuna ina sauraro (dakon) farkawarsu har sai da alfijiri ya bullo suka farka suka sha daga gorar madarar nan da na yi tattalinta gare su. Ya Allah! Idan dai na aikata haka ne domin neman yardarKa (ladarKa) Ka buda mana wata kofa daga wannan falale da ya rufe mu cikin kogo. Sai (Allah) Ya buda musu wata karamar kofar da ba za su iya fita ba daga gare ta.” Annabi (SAW) ya ce, “Sai daya daga cikinsu ya ce, “Ya Allah! Ya kasance ina da wata ’yar baffana wadda ta kasance na fi so daga mutane sai na yi nufin saduwa da ita sai ta ki yarda da ni. Har wasu shekaru suka shude masu yawa, wata rana sai ta zo gare ni domin wata bukata a wata shekarar tsananin yunwa sai na ba ta Dinari dari da ashirin saboda ta yarda in sadu da ita, sai ta yarda har lokacin da na kai zan sadu da ita, sai ta ce: “Ban halatta maka ka bude likin (rufin farjina) face da hakkinsa (aure). Sai na yi tunanin laifin aikata haka saboda auka (fadawa) mata da jima’i sai na juya (fasa) daga gare ta. Alhali ita ce fiyayyar mace da nake so daga mutane na bar mata kyautar zinarin da na ba ta. Ya Allah! Idan na aikata haka saboda neman yardar fuskarKa ne, Ka kwaranye (bude) mana daga halin da muke ciki, sai falalen ya janye kadan amma duk da haka ba za su iya fita ba.” Annabi (SAW) ya ce, “Na ukunsu ya ce, “Ya Allah! Hakika na taba yin jinga da wasu mutane sai na ba su ladar jingarsu face wani mutum guda daga cikinsu ya bar nasa, ya tafi. Sai na rika noman ’ya’yana itace da kudin jingarsa har dukiyarsa ta yawaita sai ya zo mini bayan wani lokacin mai tsawo, ya ce, “Ya Bawan Allah! Na zo ka ba ni ladar jingata,” sai na ce, masa tafi ka kama dukkan abin nan da kake gani na rakuma da shanu da tumaki da bayi.” Sai ya ce, “Shin kana yin mini ba’a ne?” Sai na ce, “Ban yi maka ba’a, sai ya karbe su duka, ya kora su bai bar mini komai ba. Ya Allah! Idan na aikata haka domin neman yardar fuskarKa ne, Ka kwaranye (bude) mana daga halin da muke ciki, sai falalen ya bude suka fita suna masu tafiya.”