Babi na Goma Sha Biyu: Rashin biyan bashi zalunci ne:

124. An karbo daga Musaddad ya ce: “Abdul-A’alah ya ba mu labari daga Ma’amar daga Hammam danMunabbihi danuwan Wahab danMunabbihi cewa: Lallai shi ya ji AbaHuraira (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Rashin biyan bashi akan lokaci zalunci ne.” BABI NA GOMA SHA UKU:Mai hakki shike da magana. An […]

Babi na Goma Sha Biyu: Rashin biyan bashi zalunci ne:
Babi na Goma Sha Biyu: Rashin biyan bashi zalunci ne:

124. An karbo daga Musaddad ya ce: “Abdul-A’alah ya ba mu labari daga Ma’amar daga Hammam danMunabbihi danuwan Wahab danMunabbihi cewa: Lallai shi ya ji AbaHuraira (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Rashin biyan bashi akan lokaci zalunci ne.”

BABI NA GOMA SHA UKU:
Mai hakki shike da magana. An karbo daga Annabi (SAW) cewa: “kin biyan bashi ga mai shi, yana halatta mutuncinsa da azabtarda shi.” Sufiyan ya ce, “Ma’anar mutuncinsa (mai binsa bashi) zai rika cewa: “Ka kuntatani,” Azabtarda shi shi ne: Tsare shi.”

125. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya ya ba mu labari daga Shu’aba daga Salmat daga Abu Salmat daga AbuHuraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Wani mutum ya je ga Annabi (SAW) yana neman ya biya bashinsa, sai ya yi mashi (Annabi) kakkausar magana. Sai sahabbanshi suka yi himmar azabtar da shi. Sai (Annabi) ya ce: “Ku kyale shi, domin hakika mai hakki shi ke da magana.”

BABI NA GOMA SHA HUdU:-
Idan mutum ya iske dukiyarsa cikin kayan gwanjo a cikin ciniki da rance da ajiya to shike hakkinshi (dukiya). Alhassan ya ce, “Idan aka yi wa mutum gwanjo (saboda bashi), kuma ya bayyana to ‘yantawarshi da cinikinsa ko sayensa ba su halatta.” Sa’id danMusayyib ya ce, “Usman ya yi hukunci da cewa: Wanda ya nemi karban hakkinsa kafin ayi gwanjo to na wannan, na shi ne. Wanda yasan kayansa da ainihinsa to shi yafi cancanta da shi.”