Babi na Goma Sha Biyu: Watannin Idi biyu ba su nukusani.

Babi na Goma Sha Biyu: Watannin Idi biyu ba su nukusani. Abu Abdullahi da Is’hak sun ce, “Koda ya kasance mai nakasa cikakke ne.” Muhammad ya ce, “Ba su haduwa dukkansu biyu masu nakasa (tawaya).” 385. An karbo daga Musaddad ya ce: “Mu’atamir ya ba mu labari ya ce, Na ji Is’hak dan Suwaid ya […]

Babi na Goma Sha Biyu: Watannin Idi biyu ba su nukusani.
Babi na Goma Sha Biyu: Watannin Idi biyu ba su nukusani.

Babi na Goma Sha Biyu:

Watannin Idi biyu ba su nukusani. Abu Abdullahi da Is’hak sun ce, “Koda ya kasance mai nakasa cikakke ne.” Muhammad ya ce, “Ba su haduwa dukkansu biyu masu nakasa (tawaya).”

385. An karbo daga Musaddad ya ce: “Mu’atamir ya ba mu labari ya ce, Na ji Is’hak dan Suwaid ya karbo daga Abdurrahman dan Abu Bakarat daga Babansa daga Annabi (SAW) Hawwala Sanad ya ce, “Musaddad ya ba ni labari, ya ce, Mu’atamir ya ba mu labari daga Khalid Haza’u ya ce, “Abdurrahman dan Abu Bakarat ya ba ni labari daga Babansa (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Watanni biyu ba su nuksani (tauyewa), watan Idin Ramadan da na Zul -Hajji.”

Babi na Goma Sha Uku:

Bisa fadar Annabi (SAW) cewa: “Ba mu rubutu kuma ba mu lissafi.”

386. An karbo daga Adamu ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Aswad dan kaisu ya ba mu labari ya ce, Sa’id dan Amru ya ba mu labari cewa: “Lallai shi ya ji dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce, daga Annabi (SAW) cewa, lallai shi ya ce: “Lallai mu, al’umma ce wadda ba mu rubutu kuma ba mu lissafi. Amma wata kamar haka da haka yake, abin da yake nufi wani lokaci ashirin da tara, wani lokaci kuma talatin.”

Babi na Goma Sha Hudu:

An hana mutum ya gabaci Ramadan da azumin yini daya ko biyu.

387. An karbo daga Muslim dan Ibrahim ya ce: “Hisham ya ba mu labari, ya ce, Yahya dan Abu Kasir ya ba mu labari daga Abu Salmata daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) cewa, lallai shi ya ce: “Kada dayanku ya gabaci Ramadan da azumin yini daya ko biyu face ga mutumin da ya kasance ke azumtar azumin nafila a wannan yini, yana iya yin azumin wannan yini.”

Babi na Goma Sha Biyar:

Da maganar Allah Madaukaki cewa: “An halatta muku daren Azumi ku sadu da matanku, su tufa ne gare ku, kuma tufafi ne gare su. Allah Ya sani lallai ku kun kasance kuna ha’intar kawunanku don haka Ya karbi tubarku (Ya yafe a kanku). Yanzu kuna iya rungumarsu ku nemi abin da Allah Ya rubuta muku. (k:2:187).”
388. An karbo daga Ubaidullahi dan Musa ya ce: “Daga Isra’ilu daga Abu Is’hak daga Barra’u (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Wani daga cikin sahabban Muhammad (SAW) ya kasance mai azumi sai lokacin buda baki ya halarto ya yi barci kafin buda baki bai ci komai ba a wannan darensa ko yininsa har sai da ya yini. Kuma lallai kaisu dan Sirmat mutumin Madina ya kasance na azumi lokacin da buda baki ya halarto sai ya je ga iyalinsa ya ce, mata: Shin akwai abinci gare ki? Ta ce, “A’a, amma bari in tafi na nemo maka. Kuma ya kasance a wannan yininsa ya yi aiki kwarai sai idonsa ya rinjaye shi da barci, matarsa ta komo gare shi ta gan shi sai ta ce: “Ka tozarta kanka,” lokacin da yini ya raba sai ya suma. Aka ba da labarinsa ga Annabi (SAW) sai wannan aya ta sauka cewa: “An halatta muku daren azumi ku sadu da matanku… sai sahabbai suka yi farin ciki da wannan, kuma aya ta sake sauka cewa: “Ku ci ku sha har sai farin zare (hasken alfijiri) ya bayyana muku daga bakin zare (duhun dare)…(k:2:187).”