Babi na Goma Sha Huxu: Fifikon wanda ya tarbiyyantar da baiwarsa:

259. An karbo daga Is’hak dan Ibrahim ya ce: “Na ji Muhammad dan Fudail ya karbo daga Mudrif daga Sha’abi daga Abu Burdah daga Abu Musa (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda duk ya kasance yana da wata kuyanga tare da shi, ya karantar da ita, kuma ya […]

Babi na Goma Sha Huxu: Fifikon wanda ya tarbiyyantar da baiwarsa:
Babi na Goma Sha Huxu: Fifikon wanda ya tarbiyyantar da baiwarsa:

259. An karbo daga Is’hak dan Ibrahim ya ce: “Na ji Muhammad dan Fudail ya karbo daga Mudrif daga Sha’abi daga Abu Burdah daga Abu Musa (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda duk ya kasance yana da wata kuyanga tare da shi, ya karantar da ita, kuma ya kyautata gare ta. Sa’an nan ya ’yantata kuma ya aure ta, yana da lada biyu (wurin Allah).”

Babi na Goma Sha Biyar:
Bisa fadar Annabi (SAW) cewa: “Bayinku ’yan uwanku ne, kuciyar da su daga abin da kuke ci.” Da fadar Allah Madaukaki cewa: “Ku bauta wa Allah kada ku hada shi da kowa kuma iyaye ku kyautata musu da ma’abuta kusanci da marayu da miskinai;…..har zuwa karshen cewa:… Allah ba Ya son mai takama mai fariya (4:36).” Abu Abdullahi (Buhari) ya ce, “Ma’abuta kusanci, ana nufin makwabci na kusa; ma’abucin gefe: ana nufin bako makusanci.”
260. An karbo daga Adamu dan Abu Iyas ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce. Wasil Al-Ahdab ya ba mu labari ya ce, “Ma’arur dan Suwaidu ya ba mu labari ya ce, na ga Abu Zarri da bawansa sanye da tufafi mai tsada iri daya. Sai muka tambaye shi game da haka, sai ya ce: “Lallai ni, wata rana na zagi wani mutum, sai ya kai ni kara wajen Annabi (SAW), sai Annabi (SAW) ya ce, mini: “Shin ka zage shi da munin uwarsa? Sa’an nan ya ce, “Lallai ’yan uwanku suke karkashinku, wadanda Allah Ya sanya su karkashin mulkinku. Duk wanda ya kasance dan uwansa na karkashin kulawarsa to ya ciyar da shi da abin da yake ci, kuma ya tufatar da shi da abin da yake daurawa. Kuma kada ya kallafa masa abin da zai gagare shi (buwaye shi), idan za ku kallafa musu abin da zai rinjaye su, to, ku taimaka musu.”
Babi na Goma Sha Shida: Hukuncin bawan da ya kyautata ibadar Mahaliccinsa kuma ya rika bin nasihar shugabansa:
261. An karbo daga Abdullahi dan Maslamah ya ce: “Daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Bawa idan ya yi nasiha (biyayya) ga shugabansa, kuma ya kyautata ibadar Mahalicinsa (Allah), ladansa zai kasance sau bibbiyu.”
262. An karbo daga Muhammad dan Kasir ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Salih daga Sha’abi daga Abu Burdah daga Abu Musa Ash’ari (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Duk mutumin da wata kuyanga (baiwa) take tare da shi, idan ya tarbiyyantar da ita, kuma ya kyautata mata karantarwa. Kuma ya ’yanta ta ya aure ta yana da lada bibbiyu. Kuma duk wani bawan da ya bayar da hakkin Allah daidai, kuma ya bayar da hakkin shugabansa yana da lada bibbiyu (a wurin Allah).”
263. An karbo daga Bishru dan Muhammad ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Yunus ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, “Na ji Sa’id dan Musayyib yana cewa: “Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Bawa na kwarai na da lada bibbiyu, ina rantsuwa da Wanda raina ke hannunSa, ba domin jihadi cikin daukaka kalmar Allah ba, da Hajji da biyayya ga uwata ba da na yi gurin in mutu ina bauta. (Wannan ya nuna muna yadda Annabi (SAW) ke nuna aikin bauta idan an yi yadda Allah Ya bayyana ba nakasa ce ba, duk da haka ba yana nufin a ci gaba da bautar da mutane ne ba).”
264. An karbo daga Is’hak dan Nasar ya ce: “Abu Usama ya ba mu labari daga A’amashi ya ce, “Abu Salih ya ba mu labari daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya ce, “Madallah ga bawan da ke kyautata ibadar Mahaliccinsa kuma ya yi biyayya ga shaugabansa.”