Babi na Goma Sha Shida

Babi na Goma Sha Shida: Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Alhali shi ne mafi tsananin husuma… (k:2:204).”:177. An karbo daga Abu Asim ya ce; “Daga Juraij daga dan Abu Mulaikatu daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), daga Annabi (SAW) ya ce, “Mutanen da Allah Ya fi fushi da su, su ne wadanda suka fi […]

Babi na Goma Sha Shida
Babi na Goma Sha Shida

Babi na Goma Sha Shida: Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Alhali shi ne mafi tsananin husuma… (k:2:204).”:
177. An karbo daga Abu Asim ya ce; “Daga Juraij daga dan Abu Mulaikatu daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), daga Annabi (SAW) ya ce, “Mutanen da Allah Ya fi fushi da su, su ne wadanda suka fi tsananin husuma.”

Babi na Goma Sha Bakwai: Laifin wanda ke fada a cikin barna alhali yana da sanin haka:
178. An karbo daga Abdul’aziz dan Abdullahi ya ce: “Ibrahim dan Sa’ad ya ba mu labari daga Salih daga dan Shihab ya ce, “Urwatu dan Zubair ya ba mu labari cewa: “Lallai Zainab ’yar Ummi Salma ta ba shi labari cewa, lallai Ummu Salmata matar Annabi (SAW) (Allah Ya yarda da ita), ta ba ta labari daga Manzon Allah (SAW) cewa: “Lallai shi ya ji wata husuma a kofar dakinsa sai ya fita gare su ya ce: “Lallai ku sani ni mutum ne, sau da yawa husuma tana zuwa gare ni, mai yiwuwa sashinku ya fi sashi iya magana har in yi tsammanin shi ne mai gaskiya, sai in yi masa hukunci (da ba shi hakkin wani), saboda haka duk wanda na ba shi hakkin wani Musulmi ba tare da hakkinsa ba, to, ya sani na ba shi yankin wuta ya karbe shi ko ya bar shi (kafin Ranar kiyama).”

Babi na Goma Sha Takwas: Laifin wanda idan ya yi husuma ba ya hakuri sai ya fajirce (ya ki hakuri ya rika miyagun zagi da cin mutuncin abokin fadarsa):
179. An karbo daga Bishiru dan Khalid ya ce: “Muhammad ya ba mu labari daga Shu’abah daga Sulaiman daga Abdullahi dan Murrat daga Masruk daga Abdullahi dan Amru dan Ass (Allah Ya yarda da su), daga Annabi (SAW) ya ce: “Abubuwa hudu wanda duk ya kasance cikinsu ya kasance munafiki. Ko ya ce, “Wanda ya kasance na da wadannan halaye hudu to ya kasance na da halin munafunci har sai ya bar su. (a) Idan ya yi magana zai yi karya (b) Idan ya yi wa’adi zai saba (c) Idan ya yi alkawari sai ya yi yaudara (d) Idan zai yi fada sai ya yi fajirci (miyagun maganganu kuma bai hakuri).”

Babi na Goma Sha Tara: kisasin (ramuwa) wanda aka zalunta idan aka samu dukiyar azzaluminsa. dan Sirin ya ce, “Sai a yi masa kisasi (ramuwa). Sai ya karanto aya cewa: “Idan za ku rama to ku rama bisa gwargwadon abin da aka cutar da ku… (k:16:126).”:
180. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shua’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Urwatu ya ba ni labari cewa: “Lallai A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Hindu ’yar Utbatu dan Rabi’a ta zo ta ce, “Ya Manzon Allah (SAW)! Lallai Abu Sufiyan mutum ne mai kwauro shin akwai laifi a gare ni idan na rika dibar abincin da zai ishe ni da iyalaina? Sai (Annabi) ya ce, “A’a ba ki da laifi idan za ki ciyar da su bisa kyautatawa (babu barna).”