Babi na Goma Sha Shida: Kamar Abin da ya gabata:

70. An karbo daga kutaiba ya ce: “Isma’il dan Ja’afar ya ba mu labari daga Musa dan Ukubatu daga Salim dan Abdullahi dan Umar daga Babansa (Allah Ya yarda da su) cewa: “Hakika Annabi (SAW) wata rana ya wuce a filinsa da ke Zul-Hulaifa a Badnil Wadi, sai aka ce, masa lallai kai kana a […]

Babi na Goma Sha Shida: Kamar Abin da ya gabata:
Babi na Goma Sha Shida: Kamar Abin da ya gabata:

70. An karbo daga kutaiba ya ce: “Isma’il dan Ja’afar ya ba mu labari daga Musa dan Ukubatu daga Salim dan Abdullahi dan Umar daga Babansa (Allah Ya yarda da su) cewa: “Hakika Annabi (SAW) wata rana ya wuce a filinsa da ke Zul-Hulaifa a Badnil Wadi, sai aka ce, masa lallai kai kana a wuri mai albarka.” Musa ya ce, “Lallai Salim ya sauka da mu inda Abdullahi yake sauka da shi, yana neman wurind a Manzon Allah (SAW) ke sauka, shi ne bisa karkashin masallaci wanda ke Badni Wadi, tsakaninsa da hanya a tsakiya ne kamar haka.”
 71. An karbo daga Is’hak dan Ibrahim ya ce: “Shu’aib dan Is’hak ya ba mu labari daga Auza’iyyu ya ce, “Yahya ya ba ni labari daga Ikramatu daga dan Abbas daga Umar (Allah Ya yarda da su) daga Annabi (SAW) ya ce: “A wani dare, wani (Jibrilu) ya zo mini daga Ubangijina lokacin yana Akik ya ce, Ka yi Sallah a wannan kwari mai albarka, ka yi niyyar Umara cikin Hajji.” (Ma’ana Umara tare da Hajji).

Babi na Goma Sha Bakwai:  Idan mai fili ya ce, “Zan zaunar da kai gwargwadon yadda Allah Ya zaunar da kai (cikin littafinSa), amma bai ambaci wani lokaci sananne ba, to bangare biyun suna nan bisa yarjejeniyarsu:

72. An karbo daga Ahmad dan Mikdam ya ce: “Fudailu dan Sulaiman ya ba mu labari ya ce, Musa ya ba mu labari ya ce, Nafi’u ya ba mu labari daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance (ya sanya jingar aikin gonakin Khaibar ga Yahudawa). Abdurrazak ya ce danJuraij ya ba mu labari ya ce, Musa danUkbah ya ba mu labari daga Nafi’u daga dan Umar cewa: “Lallai Umar dan Khaddab (Allah Ya yarda da shi), ya kori Yahudawa da Nasara daga kasar Hijaz, kuma alhali Manzon Allah (SAW) ya kasance lokacin da ya samu rinjayen a kan mutanen Khaibara da yaki, ya yi nufin fitar da Yahudawa daga cikinta, saboda lokacin kasar ta kasance tunda aka ci su da yaki ta Allah ne da ManzonSa (SAW) da Musulmi. Don haka ya yi nufin korar Yahudawa daga cikinta sai Yahudawa suka roki Manzon Allah (SAW) da ya zaunar da su cikinta, kuma ya sanya su masu lura da gonankin suna da rabin abin da aka samu daga amfanin gona. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Za mu zaunar da ku cikinta bisa ga haka gwargwadon abin da muka so. Sai suka zauna cikinta har sai da Umar ya kore su zuwa Taima’u da Ariha.

Babi na Goma Sha Takwas: Sahabban Annabi (SAW) sun kasance suna rabon gona a tsakanin sashinsu da sashi bisa ’ya’yan itace:
73. An karbo daga Muhammad dan Mukatil ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Auza’iyyu ya ba mu labari daga Abu Najjashi bawan Rafi’u dan Khadija ya ce, “Na ji Rafi’u dan Khadija dan Rafi’u ya ce, daga Baffansa Zuhair dan Rafi’u, Zuhairu ya ce: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya hana mu game da abin da ke samar da taimako a tsakaninmu (na yaudara). Na ce, “Abin da Manzon Allah (SAW) ya ce, shi ne gaskiya.” Ya ce, “Manzon Allah (SAW) wata rana ya kira ni ya ce: “Me kuke aikatawa game da gonakinku? Na ce, “Muna jingarsu a bisa gabar kogi, kuma muna yi bisa awuski daga dabino da sha’iri.” Ya ce, “Kada ku aikata haka, ku shuka ta da kanku, ko ku ba wani ya shuka da kansa, ko kuma ku bar ta haka babu shuka.” Rafi’u ya ce, “Mun ji kuma mun yi biyayya.”