Babi na Goma Sha Shida: Kamar Abin da ya gabata: (1)
74. An karbo daga Ubaidullahi dan Musa ya ce: “Auza’iyyu ya ba mu labari daga Adda’u daga Jabir (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Sun kasance suna noma gonaki bisa jingar daya cikin uku na amfanin gona, ko daya cikin hudu ko kuwa rabi.” Sai Annabi (SAW) ya ce, “Wanda duk ya kasance yana […]
74. An karbo daga Ubaidullahi dan Musa ya ce: “Auza’iyyu ya ba mu labari daga Adda’u daga Jabir (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Sun kasance suna noma gonaki bisa jingar daya cikin uku na amfanin gona, ko daya cikin hudu ko kuwa rabi.” Sai Annabi (SAW) ya ce, “Wanda duk ya kasance yana da wata gona to ya shuka ta da kansa ko ya bayar da kyautarta ga wani ya noma ko idan ba zai aikata haka ba, to ya rike gonarsa.” Rabi’u dan Nafi’u Abu Tauba, ya ce, “Mu’awiyya ya ba mu labari daga Yahaya daga Abu Salmata daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Wanda ya kasance na da wata kasar noma to ya shuka ta da kansa ko ya bayar da ita ga wani dan uwansa, idan ya kiya to ya rike gonarsa.”
75. An karbo daga kabisata ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Amru ya ce; na ambace shi ga dawus sai ya ce: “Ya noma (wato yana iya bayar da hayar gona),” dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Hakika Annabi (SAW) bai hana ba game da haka. Amma dai ya ce, game da haka: Da dai dayanku zai ba wa dan uwansa kyauta to shi ya fi alheri bisa ga ya karbi wani abu sananne.”
76. An karbo daga Sulaiman dan Harbu ya ce; “Hammadu ya ba mu labari daga Ayyub daga Nafi’u cewa: “Lallai dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya kasance yana hayar gonarsa a zamanin Annabi (SAW) da Abubakar da Umar da Usman har lokacin shugabancin Mu’awiyya. Sa’an nan sai aka karbo labari daga Rafi’u dan Khadija cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya hana game da hayar gona.” Sai dan Umar ya tafi zuwa ga Rafi’u na tafi tare da shi (in ji Nafi’u) ya tambaye shi, sai ya ce: “Annabi (SAW) ya hana game da hayar gona.” Sai dan Umar ya ce, “Hakika ko ka san muna hayar gonakinmu a zamanin Manzon Allah (SAW) da abin da ke bisa Arbi’a gaban kogi kuma bisa wasu ’ya’yan baure sanannu.”
77. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari ya ce, daga Ukailu daga dan Shihab ya ce, Salim ya ba ni labari cewa: “Lallai Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce, “Na kasance mafi sani cewa a zamanin Manzon Allah (SAW) lallai kasar noma ana hayarta, sa’an nan Abdullahi ya ji tsoron kada Annabi (SAW) ya farar da wani abu cikin haka wanda bai san shi ba. Sai ya bar yin hayar gonar.”
Babi na Goma Sha Tara: Hayar kasa da Zinari da azurfa. dan Abbas ya ce: “Abin da ya fi zama abin misali daga abin da kuke aikatawa shi ne da dai za ku bayar da hayar kasar noma bisa ga abin da aka girba a cikin shekara”:
78. An karbo daga Amru dan Khalid ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Rabi’ata dan Abu Abdurrahman daga Hanzalata dan kaisu daga Rafi’u dan Khadija ya ce, “Baffanina sun ba ni labari cewa: “Lallai su, sun kasance suna bayar da hayar gonaki a zamanin Annabi (SAW) daga abin da ya tsiro daga gabar kogi, koda wani abin da mai gonar ke togiya da shi. Sai Annabi (SAW) ya hana game da haka, sai na ce, wa Rafi’u: “To mene ne laifin idan hayar ta kasance bisa kudi ne na Zinari da Dirhami? Sai Rafi’u ya ce, “Babu laifin game da yin haya bisa Zinari da Dirhami.” Laisu ya ce, “Abin da aka hana kuma game da haka shi ne abin da mazowa sanin Halal da Haram suka duba cikinsa ba su halatta shi saboda abin da suka lura da shi na hadarurruka.”