BABI NA GOMA SHA TARA:-

Abinda aka hana game da tozarta dukiya. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Allah ba Ya son barna (2:205). Kuma ba shi gyara ayyukan masu fasadi (barna) 10:81). Da fadarsa cewa: “Shin sallolinka (ibadarka) ke umurtanka da mu bar bautawa abinda iyayenke bautawa, ko mu aikata abinda muke so cikin dukiyarmu (11:817).” Da fadar Allah Madaukaki […]

BABI NA GOMA SHA TARA:-
BABI NA GOMA SHA TARA:-

Abinda aka hana game da tozarta dukiya. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Allah ba Ya son barna (2:205). Kuma ba shi gyara ayyukan masu fasadi (barna) 10:81). Da fadarsa cewa: “Shin sallolinka (ibadarka) ke umurtanka da mu bar bautawa abinda iyayenke bautawa, ko mu aikata abinda muke so cikin dukiyarmu (11:817).” Da fadar Allah Madaukaki cewa: “Kada ku ba wawayea dukiyarku- (4:5).” Tsaro ke cikin haka, kuma da bayanin abinda aka hana game da yaudara.
            
129. An karbo daga Abu Nu’aim ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Abdullahi danDinar ya ce: “Na ji danUmar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Wani mutum ya ce wa Annabi (SAW) lallai ni: Ana yaudara ta cikin ciniki,” sai (Annabi) ya ce, “Idan zaka yi ciniki ka ce: “Banda yaudara,” sai mutumin ya kasance yana fadin haka.

130. An karbo daga Usman ya ce: “Jarir ya ba mu labari daga Mansur daga Sha’abi daga Warrad bawan Mughira danShu’aba daga Mughirat danShu’aba ya ce, “Annabi (SAW) ya ce, “Hakika Allah ya haramta muku gudun iyaye; da turbude ‘ya’yanku mata; da kin bayar da hakkin wani ta hanyar kyautatawa da yawan roko; kuma ya hana muku jita-jita (magana mara tabbaci); da yawan tambaya; da barnar dukiya.”

BABI NA ASHIRIN:-
Bawa mai tsaron dukiyar shugabansa, ba shi yin wani aiki sai da izinisa.

131. An karbo Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Salim dan Abdullahi ya ba ni labari daga Abdullahi danUmar (Allah Ya yarda da su), cewa: Lallai shi Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Dukkanku masu kiwo ne, kuma kowa za’a tambaye shi game da abin kiwonsa, shugaba mai kiwo ne kuma shi wanda za’a tambaya ne game abin kiwonsa. Mutum cikin iyalansa mai kiwo ne kuma za’a tambaye shi game da abin kiwonsa. Mace cikin gidan mijinta makiyayi ce, kuma za’a tambaye ta game da abin kiwonta. Mai aiki makiyayi ne cikin dukiyar shugabansa za’a tambaye shi game da abin kiwonsa.” Ya ce, “Na ji wadannan daga Manzon Allah (SAW) ina tsammani ya ce: “Mutum cikin dukiyan babansa mai kiwone kuma za’a tambaye shi game da abin kiwonsa, kuma dukkanku makiyaya ne kuma dukkanku za’a tambaye ku game da abin kiwonku.”