Babi na Goma Sha Uku (2)

Babi na Goma Sha Uku: Ladar wanda ya sanya kansa bisa yin jingar dako, sa’an nan ya yi sadaka da abin da ya samu da bayanin sakamakon ’yan dako:13. An karbo daga Sa’id dan Yahya dan Sa’id ya ce: “Babana ya ba mu labari ya ce, A’amashi ya ba mu labari daga Shakik daga Abu […]

Babi na Goma Sha Uku (2)
Babi na Goma Sha Uku (2)

Babi na Goma Sha Uku: Ladar wanda ya sanya kansa bisa yin jingar dako, sa’an nan ya yi sadaka da abin da ya samu da bayanin sakamakon ’yan dako:
13. An karbo daga Sa’id dan Yahya dan Sa’id ya ce: “Babana ya ba mu labari ya ce, A’amashi ya ba mu labari daga Shakik daga Abu Mas’ud mutumin Madina (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya kasance idan ya yi umarni da yin sadaka sai dayanmu ya tafi zuwa kasuwa ya yi dako har ya samo muddi (mudu) daya (na abinci). Kuma lallai dayanmu yakan kasance yana da Dirhami dubu (ta hanyar dako, ko ya ce yanzu akwai mai Dirhami dubu). (Shakik,) ya ce: “Ina tsammani shi (Abu Mas’ud) da kansa yake cewa wani daga cikinmu.”

Babi na Goma Sha Hudu:
Ladar dan dako (dan alaro). dan Sirin da Adda’u da Ibrahim da Alhassan ba su ga laifin ladar (jingar) dillali ba. dan Abbas ya ce: “Babu laifi mutum ya ce, “Sayar da wannan tufafi abin da ya karu bisa kaza da kaza to na bar shi gare ka. dan Sirin ya ce, “Idan ka ce, sayar da shi bisa farashin kaza na riba idan wani abu ya karu to naka ne, ko ya ce, riba na tsakanina da kai.” Annabi (SAW) ya ce, “Musulmi suna a bisa sharuddansu.”
14. An karbo daga Musaddad ya ce: “Abdul Wahid ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga dan dawus daga Babansa daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya hana game da taryar ayarin ’yan kasuwa daga wajen gari, kafin su iso kasuwa. Kuma ya hana mutumin birni ya sayar wa mutumin kauye da kaya.” Sai na ce, ya dan Abbas mene ne ma’anarsa bisa cewa: “Kada mutumin birni ya sayar wa mutumin kauye.” dan Abbas ya ce: “Ma’anarsa ita ce: Kada ya zamo (kasance) masa kamar dillali.”