Babi na Hudu:
Idan mutum ya yi jinga da wani mutum bisa aikin kwana uku, ko bayan wata daya, ko bayan shekara daya ya halatta. Kuma su biyu suna a bisa wannan sharadinsu wanda suka shardanta shi har idan lokaci yayi: 5. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ukailu ya […]
Idan mutum ya yi jinga da wani mutum bisa aikin kwana uku, ko bayan wata daya, ko bayan shekara daya ya halatta. Kuma su biyu suna a bisa wannan sharadinsu wanda suka shardanta shi har idan lokaci yayi:
5. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ukailu ya ce, dan Shihab ya ce, Urwata dan Zubair ya ba ni labari cewa: Lallai A’isha matar Annabi (SAW) (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Manzon Allah (SAW) da Abubakar sun yi jinga da wani mutum daga kabilar Dailu kwararre ne bisa jagoranci, kuma shi yana bisa addinin kafiran kuraishawa. Sai suka ba shi taguwarsu suka yi alkwarin haduwa da shi a kogon Sauru bayan kwana uku ya zo da taguwarsu a subahin dare na uku.”
Babi na Biyar: Yin jinga a lokacin yaki:
6. An karbo daga Yakub dan Ibrahim ya ce: “Isma’il dan Ulayyata ya ba mu labari ya ce, dan Juraij ya ba mu labari, ya ce, Adda’u ya ba ni labari daga Safawan dan Ya’ala daga Ya’ala dan Umayyata (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Na yi yaki tare da Annabi (SAW) yakin Usrah (Tabuka) kuma shi ne fiyayyen aikin da ke cikin raina. Kuma ya kasance ina da wani mai aiki (jinga) sai ya yi fada da wani mutum, dayansu ya ciji yatsar dan uwansa, sai ya fisge yatsunsa har sai da ya cire masa hakorin gaba ya fadi. Sai ya tafi zuwa ga Annabi (SAW) yana kara, sai (Annabi SAW) ya ce, babu fansar wannan hakori. Ya ce, “Shin kana son ya sanya yatsunsa cikin bakinka domin ka rama? (Mai ruwaya) ya ce, “Ina tsammanin (Annabi SAW) ya ce, “Kamar cizon rakumi.” dan Juraij ya ce, Abdullahi dan Abu Mulaikatu ya ba ni labari daga Kakansa da misalin wannan siffar cewa: “Lallai wani mutum ya ciza yatsar wani mutum, har ya fitar masa da hakorin gaba, sai Abubakar ya kore biyan diyyar wannan yatsa.”
Babi na Shida:
Idan mutum ya kulla jinga da wani, kuma ya bayyana masa ajalin kuma bai bayyana masa aikin ba shin haka ya yi? Bisa fahimtar maganar Allah Madaukaki cewa: “Hakika ni, ina son in aurar maka da daya daga cikin ’yata wadannan…har zuwa bisa cewa…Allah Wakili ne bisa ga abin da na ke fadi. (k:28:27-28). Da Larabci ana cewa, wane ya yi jinga da wane, idan ya ba shi ladar jinga. Kuma ana fadin haka cikin ta’aziyya (gaisuwar mutuwa) cewa, “Allah Ya ba ka ladar hakuri.”
Babi na Bakwai: Idan mutum ya yi jinga da wani bisa gyaran ganuwa (katanga) da ya yi kusan karyewa, ya halatta:
7. An karbo daga Ibrahim dan Musa ya ce: “Hisham dan Yusuf ya ba mu labari cewa, lallai dan Juraij ya ba su labari ya ce, Ya’ala dan Muslim ya ba ni labari da Amru dan Dinar daga Sa’id dan Jubair ya ce, dayansu yana kari bisa ga maganar abokinsa da wasunsu ya ce, “Na ji shi yana ba da labari daga Sa’id ya ce, dan Abbas (Allah Ya yarda da su) ya fada min cewa: “Ya ce, Ubayyu dan Ka’ab ya ba ni labari ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya ce, (game da labarin Musa (AS) da Khadir) “Sai suka tafi suka samu (iske) wani kango wanda yake nufin faduwa…” Sa’id ya ce, “Sai Khadir ya gyara shi da hannunsa kamar haka, ya daukaka hannunsa ya mikar da shi.” Ya’ala ya ce, “Ina tsammani lallai Sa’id ya ce, “(Musa) ya ce, “Da ka so da ka karbi jingar (ladan) aikinka a kansa.” Sa’id ya ce, “yana nufin ladar jinga don mu sayi abincin da za mu ci.”