Babi na Sittin da Tara: Azumin Ashura (10 ga Muharram):
457. An karbo daga Abu Asim ya ce: “Daga Umar dan Muhammad daga Salim daga Babansa (RA) ya ce: “Annabi (SAW) ya ce, “Wanda ya so ya yi azumin Ranar Ashura.” 458. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Urwata dan Zubair ya ba ni labari […]
457. An karbo daga Abu Asim ya ce: “Daga Umar dan Muhammad daga Salim daga Babansa (RA) ya ce: “Annabi (SAW) ya ce, “Wanda ya so ya yi azumin Ranar Ashura.”
458. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Urwata dan Zubair ya ba ni labari cewa: “Lallai A’isha (RA), ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance ya yi umarni da yin azumin Ranar Ashura, lokacin da aka farlanta Ramadan, sai ya kasance wanda ya so ya yi azumin, wanda ya so ya bari (ya ci abinci).”
459. An karbo daga Abdullahi dan Maslamata ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Hisham dan Urwata daga Babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Ranar Ashura (10 ga watan Muharram) kuraishawa sun kasance suna azumtarsa a Jahiliyya. Kuma Manzon Allah (SAW) ya kasance yana azumtarsa. Lokacin da ya isa (kaura) zuwa Madina ya azumce shi, kuma ya yi umarni da azumtarsa. Lokacin da aka farlanta Ramadan sai ya bar azumin yinin Ashura, wanda ya yi azuminsa, wanda ya so ya bar shi (ya ci abincinsa).”
460. An karbo daga Abdullahi dan Maslamata ya ce: “Daga Malik daga dan Shihab daga Humaid dan Abdurrahman cewa: “Lallai shi ya ji Mu’awiyya dan Abu Sufiyan (RA) a Ranar Ashura a shekarar aikin Hajji yana a bisa mumbari yana cewa: “Ya ku mutanen Madina! Ina malamanku? Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Wannan yinin Ashura ne, Allah bai wajabta muku azumtarsa ba, amma ni ina azumin. Wanda ya so ya yi azumi, wanda ya so ya ci abinci.”
461. An karbo daga Abu Ma’amar ya ce: “Abdulwaris ya ba mu labari ya ce, Ayyub ya ba mu labari ya ce, Abdullahi dan Sa’id dan Jubair ya ba mu labari daga Babansa daga dan Abbas (RA) ya yarda da su, ya ce: “Annabi (SAW) ya isa (kaura) zuwa Madina ya ga Yahudawa suna azumin Ashura, sai ya ce, “mene ne wannan? Suka ce, “Wannan yini ne na kwarai, kuma yini ne da Allah Ya kubutar da Bani Isra’il daga makiyinsu, don haka ya azumce shi.” Sai (Annabi) ya ce, “Ni na fi cancantar Musa da ku, sai ya rika azumtarsa, ya yi umarni da yin azuminsa.”
562. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Abu Usama ya ba mu labari daga Abu Umais ya ce, daga kaisu dan Muslim daga darik dan Shihab daga Abu Musa (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Ranar Ashura ta kasance Yahudawa na girmama ta kamar Idi. Sai Annabi (SAW) ya ce, “Ku yi azuminsa ku ma.”
563. An karbo daga Ubaidullahi dan Musa ya ce: Daga dan Uyainata daga Ubaidullahi dan Abu Zaid daga dan Abbas (RA), ya ce: “Ban ga Annabi (SAW) yana neman yin wani azumin wani yini da ya fifita shi a kan waninsa ba face wannan yini, wato yinin Ashura da wannan wata yana nufin watan Ramadan.”
564. An karbo daga Almakkiyu dan Ibrahim ya ce: “Yazid dan Abu Ubaidu ya ba mu labari daga Salmata dan Akwa’u (RA) ya ce: “Annabi (SAW) ya umarci wani mutum daga cikin kabilar Aslam da ya yi shela ga mutane cewa: “Wanda ya riga ya ci abinci to ya cika sauran yininsa (da kamun baki). Wanda bai ci komai ba, to ya yi azumi domin lallai yau ne ranar Ashura.”