Babi na Takwas:

Babi na Takwas:Yafewar wanda aka zalunta. Bisa fadar Allah Madaukakin Sarki cewa: “Idan kun bayyana alheri ko kun boye ko kuka yafe game da mummuna (zalunci), hakika Allah Ya kasance Mai yafiya Mai iko (k:4:149).” Da fadarSa cewa: “Sakamakon mummuna da mai muni misalinta, wanda ya yafe kuma ya yi sulhu, to ladarsa na ga […]

Babi na Takwas:
Babi na Takwas:

Babi na Takwas:
Yafewar wanda aka zalunta. Bisa fadar Allah Madaukakin Sarki cewa: “Idan kun bayyana alheri ko kun boye ko kuka yafe game da mummuna (zalunci), hakika Allah Ya kasance Mai yafiya Mai iko (k:4:149).” Da fadarSa cewa: “Sakamakon mummuna da mai muni misalinta, wanda ya yafe kuma ya yi sulhu, to ladarsa na ga Allah. Lallai Shi Allah ba ya son azzalumai. Wanda ya nemi taimako (yafe) bayan zaluncinsa. Wadannan ba su wata hanya a kansu (na neman sakayya). Amma dai hanya na ga wadanda suke zaluntar mutane kuma suna neman yin zalunci a cikin kasa ba tare da gaskiya ba. Wadannan suna da wata azaba mai tsanani. Amma wanda ya yafe ya gafarta, lallai haka na daga cikin manyan al’amura. Za ka ga azzalumai lokacin da suka azaba za su rika cewa: Shin zuwa ga magargadan ko akwai mafita (wurin gudu zuwa duniya)… (k:42: 40-44).”
Babi na Tara: Zalunci duffai ne Ranar kiyama:
167. An karbo daga Ahmad dan Yunus ya ce: “Abdul’aziz Majishiyyu ya ba mu labari ya ce, Abdullahi dan Dinar ya ba mu labari daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), daga Annabi (SAW) ya ce: “Zalunci duffai ne Ranar kiyama.”
Babi na Goma: Jin tsoro da kiyayewa daga addu’ar wanda aka azzalunta:
168. An karbo daga Yahya dan Musa ya ce: “Waki’u ya ba mu labari ya ce, Zakariya dan Is’hak mutumin Makka daga Yahya dan Abdullahi dan Saifi daga Abu Ma’abad bawan dan Abbas daga Abdullahi dan Abbas (Allah Ya yarda da su) cewa: “Hakika Annabi (SAW) ya aika da Mu’azu zuwa Yemen ya ce: “Ka ji tsoron addu’ar wanda aka zalunta, domin lallai ita (addu’ar) ba ta da wani shamaki tsakaninta da Allah.”
Babi na Goma Sha daya: Shin idan mutum na da wani abin zalunci wurin wani ya hatta masa, shin zai iya bayyana zaluncinsa?:
169. An karbo daga Adamu dan Abu Iyas ya ce: “dan Abu Zi’ib ya ba mu labari ya ce, Sa’id Makburi daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce; “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya kasance yana da wani abin zalunci ga dan uwansa daga mutuncinsa ko dai wani abu, to ya halatta masa shi yau, kafin ya zamo Zinari ko Dirhami. Domin idan ya kasance masa na da wani aikin kwarai sai a karba daga gare shi gwargwadon zaluncinsa (a biya wanda ya zalunta da shi). Idan kuwa ba ya da wasu kyawawan aiki sai a diba daga munanan ayyukan abokinsa (wanda ya zalunta) sai a dora a kansa.” Abu Abdullahi (Buhari) ya ce, Isma’il dan Abu Uwais ya ce: “An dai ambaci Makburi saboda ya sauka kusa da farfajiyar makabarta ne. Abu Abdullahi (Buhari) ya ce, Sa’id al-Makburi shi ne bawan kabilar Laisu shi ake kira da sunan Sa’id dan Abu Sa’id, sunan Abu Sa’id Kaisan.
Babi Na Goma Sha Biyu: Idan mutum ya halatta (yafe) game da abin da aka zalunce shi ba ya da ikon komawa wajen neman hakkinsa:
170. An karbo daga Muhammad ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Hisham dan Urwata daga Babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita) cewa: “Game da fassarar wannan aya: “Idan wata mace ta ji tsoron wani abu na sabani ko rabuwa daga mijinta (k:4:128), sai ta ce: “Wani mutum yakan ji bai son matarsa har ya yi nufin sakinta, sai ta rika cewa masa: Na bar maka dukkan sha’anina na hakki kada ka sake ni.” Sai Allah Ya saukar da wannan aya.