Babi na Takwas: Hukuncin bashi:

35. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ukailu daga dan Shihab daga Abu Salmata daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya kasance ana zuwa masa da mutumin da ya mutu, alhali ana binc sa bashi, sai (Annabi) ya tambaya, shin […]

Babi na Takwas: Hukuncin bashi:
Babi na Takwas: Hukuncin bashi:

35. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ukailu daga dan Shihab daga Abu Salmata daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya kasance ana zuwa masa da mutumin da ya mutu, alhali ana binc sa bashi, sai (Annabi) ya tambaya, shin ya bar wani abin biyan bashinsa? Idan aka ba shi labari cewa, lallai shi mamacin ya bar wani abin da zai biya masa bashi, sai ya yi masa Sallah. Idan ba haka ba, sai (Annabi) ya ce, wa Musulmi: “Ku yi wa abokinku Sallah,” lokacin da Allah Ya yi masa (Annabi) budin cin nasara da wasu yake-yake, sai ya ce: “Ni ne fiyayyen wanda ya cancanci biyan bashin muminai daga kawunansu, wanda ya mutu daga cikin uminai ya bar bashi biyan bashinsa yana kaina, wanda ya bar dukiya yana ga magadansa.”
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.
Littafin Wakalat (wakilci):
Babi na Farko: Wakilcin abokin hulda, shi ne tarayya a cikin rabon hakki ko waninta. Hakika Annabi (SAW) ya yi tarayya da Aliyu a cikin hadayarsa. Sa’an nan ya yi umarni da raba ta (bayarwa ga jama’a):
36. An karbo daga kabisa ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga dan Abu Najih daga Mujahid daga Abdurrahman dan Abu Lailah daga Aliyu (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya umurce (wakilta) ni, in yi sadaka da mayafin taguwar hadaya wadda aka soke da fatunta.”
37. An karbo daga Amru dan Khalid ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Yazid daga Abul Khair daga Ukbatu dan Amir (Allah Ya yarda da shi) cewa: Lallai Annabi (SAW) ya ba shi wasu tumaki domin ya raba su ga sahabbansa sai wani dan tunkiya ya saura, ya ambata shi ga Annabi (SAW) ya ce: “Ka yi layya da shi ga kanka.”
Babi na Biyu: Idan Musulmi ya wakilta jarumin kafirin da ake yaki da shi a gidajen yaki ko gidan Musulunci ya halatta:
38. An karbo daga Abdul’aziz dan Abdullahi ya ce: “Yusuf dan Majishiyyu ya ba mu labari daga Salih dan Ibrahim dan Abdurrahman dan Aufu daga Babansa daga kakansa Abdurrahman dan Aufu (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Na rubuta wata takardar alkawari tsakanina da Umayyatu dan Khalfu bisa alkawarin zai tsare mini dukiyata a Makka, shi kuma zan tsare masa dukiyarsa a Madina, lokacin da na ambaci Rahman cikin sunana, sai ya ce, “Ban san Rahman ba, ka rubuta mini wanda ya kasance a Jahiliyya, sai na rubuta masa Abdu Amri. Lokacin da yinin Badar ya kasance sai na fita zuwa ga wani dutse don in lura da shi lokacin da mutane suka yi barci. Sai Bilal ya gan shi ya fita bai zame ba face sai da ya kai mazaunan mutanen Madina, sai (Bilal) ya ce, Umayyatu dan Khalfu ne, ya ce, “Ban tsira ba, idan Umayyatu ya kubuta,” sai (Bilal) ya fito tare da wasu jama’a na garin Madina suna neman inda muke. Lokacin da na ji tsoron kada su riske mu sai na halifantar da dansa domin ya shagaltar da su, sai suka kashe shi, kuma suka ki barinmu suna nemanmu, kuma (Umayyatu) mutum ne mai nauyin jiki, lokacin da suka riske mu sai nace masa, sunkuya! Sai ya sunkuya, sai na jefo kaina gare shi domin in tsare shi, sai suka rufe shi da takkuba daga karkashina har sai suka kashe shi, wani daga cikinsu ya samu kafa ta da takobinsa. Abdurrhaman dan Aufu ya kasance yana nuna mana alamar tabo a bayan duddugensa.” Abu Abdullah (Buhari) ya ce, “Yusuf ya ji daga Salih, Ibrahim kuma ya ji daga Babansa.