Babi na Takwas: Jinga zuwa rabin yini (yin ladar aikin kodago zuwa rabin yini):

8. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Hammadu ya ba mu labari, daga Ayyub daga Nafi’u daga dan Umar (RA), daga Annabi (SAW) ya ce: “Misalinku da misalin wadanda aka ba wa littafi gabaninku kamar mutumin da ya yi jinga ne da wasu masu aiki (kwadago) bisa cewa: Wanda ya yi mini aiki […]

Babi na Takwas: Jinga zuwa rabin yini (yin ladar aikin kodago zuwa rabin yini):
Babi na Takwas: Jinga zuwa rabin yini (yin ladar aikin kodago zuwa rabin yini):

8. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Hammadu ya ba mu labari, daga Ayyub daga Nafi’u daga dan Umar (RA), daga Annabi (SAW) ya ce: “Misalinku da misalin wadanda aka ba wa littafi gabaninku kamar mutumin da ya yi jinga ne da wasu masu aiki (kwadago) bisa cewa: Wanda ya yi mini aiki daga safe zuwa rabin yini yana ladar kiradi? Sai Yahudawa suka yi aiki, sa’an nan ya ce, “Wane ne zai yi mini aiki daga rabin yini zuwa Sallar La’asar bisa jingar kiradi? Sai Nasara suka yi aiki, sa’an nan ya ce: “Wane ne zai mini aiki daga La’asar zuwa buyar rana bisa ladar (jinga) kiradi biyu? To ku ne kamarsu (jama’ar karshe). Sai Yahudu da Nasara suka yi fushi suka ce: “Me ya sanya muka fi yawan aiki amma kuma muke da karancin lada (sakamako)? (Allah) zai ce, “Shin Na tauye muku wani abu daga hakkinku ne? Sai suce “A’a,” Sai Ya ce, “Wannan ita ce, fifitawaTa ina bayar da ita ga wanda Na so.”

Babi na Tara: Jinga zuwa Sallar La’asar:

9. An karbo daga Isma’il dan Abu Uwais ya ce: “Malik ya ba ni labari daga Abdullahi dan Dinar bawan Abdullahi dan Umar daga Abdullahi dan Umar dan Khaddab (RA), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Hakika misalinku da Yahudu da Nasara (Kiristoci) kamar wani mutum ne da ya yi jinga da wasu ma’aikata. Ya ce, “Wa zai yi mini aiki zuwa rabin yini bisa kiradi daidai? Sai Yahudu suka yi aiki zuwa rabin yini bisa jingar (lada) kiradi daidai. Sa’an nan Nasara (Kiristoci) suka yi aiki bisa jingar kiradi daidai, sa’an nan ku ne wadanda za ku yi aiki daga Sallar La’asar zuwa buyar rana bisa jingar kiradi bibbiyu. Sai Yahudu da Nasara su yi fushi su ce: “Mu muka fi yawan aiki amma muka fi karancin lada (sakamako).” (Allah) Ya ce, “Shin na zalunce ku wani abu daga hakkinku? Suka ce, “A’a.” Ya ce, “Wannan ita ce fifitawaTa (falala) ina bayarwa da ita ga wanda Na so.”

Babi na Goma: Laifin wanda ya hana (ki biyan) hakkin dan kwadago:

10. An karbo daga Yusuf dan Muhammad ya ce: “Yahya dan Sulaim ya ba ni labari daga Isma’il dan Umayya daga Sa’id dan Abu Sa’id daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) ya ce, “Allah Madaukaki Ya ce: “Mutum uku Ni ne mai yin husuma da su, (abokan gabaNa) Ranar kiyama: (1) Mutumin da aka hada shi da Ni ya yi yaudara. (2) Da mutumin da ya sayar da dan Adam mai ’yanci ya ci kudinsa. (3) Da mutumin da ya yi jinga da wani mutum, ya gama masa aiki bai biya shi ladarsa ba.”