Babi na Takwas: Salami a cikin dabba har zuwa taguwar ta haifi abin da ke cikinta ta shayar da shi:

Babi na Takwas: Salami a cikin dabba har zuwa taguwar ta haifi abin da ke cikinta ta shayar da shi: 696. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Juwairiyyata ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Mutane sun kasance suna sayar da rakuma bisa yarjejeniya Habalal […]

Babi na Takwas: Salami a cikin dabba har zuwa taguwar ta haifi abin da ke cikinta ta shayar da shi:
Babi na Takwas: Salami a cikin dabba har zuwa taguwar ta haifi abin da ke cikinta ta shayar da shi:

Babi na Takwas: Salami a cikin dabba har zuwa taguwar ta haifi abin da ke cikinta ta shayar da shi:

696. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Juwairiyyata ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Mutane sun kasance suna sayar da rakuma bisa yarjejeniya Habalal Habal. Sai Annabi (SAW) ya hana game da shi.” Nafi’u ya fassara ma’anarta da cewa: “Ita ce har sai taguwar ta haife abin da ke cikinta (ga mai sayarwa) ta shayar.”

 Littafain Kamun Shufu’ah:
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai.
Salami a cikin Shufu’ah:

Babi na Farko: Shufu’a na aukuwa ne bisa ga kayan da ba a raba ba. Idan rabo ya auku bisa dokoki (iyakoki) to babu shufu’a (kamun ciniki na makwabtaka):

697. An karbo daga Musaddad ya ce: “Abdulwahid ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Zuhuri daga Abu Salmata dan Abdurrahman daga Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya yi hukunci da kamun shufu’ah a cikin kowane abu matukar ba a raba ba, amma idan ta fada cikin rabon iyaka, ko hanya ta rarraba, to babu kamun shufu’ah.”

Babi na Biyu:
Makwabci ya kamata ya fara sanar da makwabcinsa bisa ga abin da yake son sayarwa kafin wani mutum. Alhakamu ya ce, “Idan makwabci ya sanar da shi (makwabci) kafin sayarwa, to ba ya da ikon kamun shufu’ah.” Sha’abi ya ce, “Wanda ya kasance aka sayar da kayan shufu’arsa bisa shaidawarsa (halartarsa) bai canza (kare hakkinsa) ba, to ba ya da ikon kamun shufu’ah”:

698. An karbo daga Almakkiyu dan Ibrahim ya ce: “dan Juraij ya ba mu labari, ya ce, Ibrahim dan Maisarata ya ba mu labari daga Amru dan Sharid ya ce: “Na tsaya a wajen Sa’ad dan Abu Wakkas sai Miswar dan Makhramata ya zo ya dora hannunsa bisa dayan kafadata lokacin da Abu Rafi’u bawan Annabi (SAW) ya zo ya ce: “Ya Sa’ad! Ka sayi gidajena biyu da ke tare da gidanka. Sai Sa’ad ya ce, “Ba zan saye su ba,” sai Miswar ya ce, ‘Wallahi za ka saye su,” Sa’adu ya ce, “Wallahi ba zan saya fiye da Dirhami dubu hudu ba, bisa zuwa wani ajali.” Abu Rafi’u ya ce, “Hakika na saye shi bisa Dinari dubu biyar ne, ba domin na ji Annabi (SAW) yana cewa: “Makwabci shi ya fi cancanta da kamun shufu’ah ba, da ban sayar maka da su bisa ga Dirhami dubu hudu ba, domin lallai ni, an sayar mini da su bisa ga Dinari dubu biyar, sai ya ba shi su bisa ga haka.”

Babi na Uku: Wane makwabci ne ya fi kusanci?:
699. An karbo daga Hajjaju ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari, -Hawwala Sanad- ya ce, Aliyu ya ba mu labari ya ce, Shabbabah ya ba mu labari ya ce, Shu’abah ya ba mu labari, ya ce, Abu Imran ya ba mu labari ya ce: “Na ji dalhat dan Abdullahi ya ce, daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa ta ce, “Na ce, ya Manzon Allah! Lallai ni, ina da makwabta biyu, wane ne daga cikinsu zan fara yi wa kyauta? Ya ce, “Wanda kofarsa ya fi kusa da ke.”