Babi na Tara:
Wakilta Shugaba ga daurin auren mace:45. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abu Hazim daga Sahlu dan Sa’ad ya ce: “Wata mace ta zo ga Manzon Allah (SAW) sai ta ce, “Ya Manzon Allah! na wakilta (bayar da kyautar) kaina gare ka. Sai wani mutum ya ce, […]
Wakilta Shugaba ga daurin auren mace:
45. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abu Hazim daga Sahlu dan Sa’ad ya ce: “Wata mace ta zo ga Manzon Allah (SAW) sai ta ce, “Ya Manzon Allah! na wakilta (bayar da kyautar) kaina gare ka. Sai wani mutum ya ce, “Ka aurar da ita gare ni,” sai ya ce, “Na aurar maka ita, da abin da ke gare na haddar Alkur’ani.”
Babi na Goma:
Idan mutum ya wakilta wani mutum, sai wakilin ya bar wani abu, wanda aka wakilta ya zartar da shi ya halatta. Idan mutum ya bayar da rance ga wani zuwa ajali sananne ya halatta. Usman dan Haisam Abu Amri ya fadi kamar haka:
46. An karbo daga Aufu ya ce: “Daga Muhammad dan Sirin daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya wakilta ni game da tsare Zakkar Ramadan (Fidiri). Sai wani mai zuwa (mutum) ya zo mini ya rika diba daga abincin sai na kama shi, na ce, “Wallahi sai na kai kararka ga Manzon Allah (SAW). Ya ce, “Lallai ni, mabukaci ne kuma ina da iyali kuma ina da bukata mai tsanani. Ya ce, “Na sake shi, na wayi gari, Annabi (SAW) ya ce, “Me wanda ka kama shi jiya ya aikata maka? Ya ce, “Ya kawo kukan bukata mai tsanani da yawan iyali sai na jikansa na fita hanyarsa. Sai (Annabi) ya ce, “Amma lallai shi ya yi maka karya, kuma zai komo.” Daga nan sai na faihimci zai komo saboda maganar Manzon Allah (SAW) gaskiya ce, lallai zai komo. Sai na yi dakonsa (fakonsa), sai ga shi ya zo yana diba daga abincin sai na kama shi, na ce, “Sai na kai ka ga Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ka bar ni, domin lallai ina da bukata, kuma gani da iyali ba zan komo ba, sai na jikansa na sake shi. Na je ga Manzon Allah (SAW) ya ce min, ya Abu Huraira! Me wanda ka kama jiya ya aikata maka? Na ce, “Ya Manzon Allah! Ya kawo kukan bukata mai tsanani da yawan iyali sai na jikansa na fita hanyarsa. Ya ce, “Amma lallai shi ya yi maka karya, zai komo, sai na sake fakonsa a ta uku, sai ya zo yana dibar abincin na kama shi, na ce, “Zan kai ka ga Manzon Allah (SAW) wannan shi ne karshen kashi na uku da kake riyawa cewa, ba za ka sake komowa ba, sa’an nan ka komo. Ya ce, “Ka bar ni zan koya maka wasu kalmomi wadanda Allah zai amfane ka da su, na ce, “Mene ne su? Ya ce, “Idan za ka kwanta bisa shimfidarka, ka karanta Ayatul Kursiyyu – Allahu La’ilaha Illa huwa Alhayyul kayyum – har zuwa karshen aya. Lallai kai, ba za ka gushe ba kana da mai tsaronka daga wajen Allah kuma Shaidan ba zai kusance ka ba har ka wayigari. Sai na fita hanyarsa da na je ga Manzon Allah (SAW) ya ce min, me wanda ka kama jiya ya aikata maka? Na ce, “Ya Manzon Allah! Ya riya cewa, zai koyar da ni wasu kalmomi wadanda Allah zai amfane ni da su, sai na fita hanyarsa. (Annabi) ya ce, “Mene ne su? Na ce, “Ya ce min idan za ka kwanta bisa shimfidarka, ka karanta Ayatul Kursiyyu daga farkonta har zuwa karshe – Allahu La’ilaha Illahuwa Alhayyul kayyum – kuma ya ce min ba za ka gushe ba face kana da mai tsaronka daga Allah, kuma Shaidan ba zai kusance ka ba har sai ka wayi gari. Kuma sun kasance abubuwan da suka fi kwadaitar da abin alheri. Sai Annabi (SAW) ya ce, “Amma lallai shi, ya yi maka gaskiya duk da yake shi makaryaci ne. Shin ko ka san da wa kake magana tun darare ukun da suka shude ya Abu Huraira! Ya ce, “A’a, ban sani ba.” Ya ce, “Shaidan ne wannan.”