Babi na Tara: Idan aka auna ko ba a auna ba a cikin biyan bashin dabino da dabino ko waninsa:
120. An karbo daga Ibrahim dan Munzir ya ce: “Anas ya ba mu labari daga Hisham daga Wahab dan Kaisan daga Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai shi ya ba shi labari cewa, hakika Babansa ya mutu ya bari ana bin sa bashi Awuski talatin na wani Bayahude. Sai Jabir ya […]
120. An karbo daga Ibrahim dan Munzir ya ce: “Anas ya ba mu labari daga Hisham daga Wahab dan Kaisan daga Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai shi ya ba shi labari cewa, hakika Babansa ya mutu ya bari ana bin sa bashi Awuski talatin na wani Bayahude. Sai Jabir ya nemi ya saurara masa sai (Bayahuden) ya ki saurara masa. Sai Jabir ya yi wa Annabi (SAW) magana don ya nema masa rangwame, Manzon Allah (SAW) ya tafi ga Bayahuden ya yi masa magana don ya karbi ’ya’yan dabinosa wanda ke tare da shi, sai (Bayahuden) ya ki karba. Sai Manzon Allah (SAW) ya shiga wajen dabinon ya yi tafiya cikinta, sa’an nan ya ce, wa Jabir cire dabinon ka auna masa kuma ka cika, ya auna masa bayan Manzon Allah (SAW) ya komo, har sai da ya cika masa Awuski talatin kuma ya rage da kamar Awuski goma sha bakwai. Sai Jabir ya tafi ga Manzon Allah (SAW) don ya ba shi labarin abin da ya saura, sai ya iske shi yana Sallar La’asar. Lokacin da ya sallame sai ya ba shi labari da abin da ya rage (saura). Ya ce, “Ka ba da labarin haka ga dan Khaddab, sai Jabir ya tafi zuwa ga Umar ya ba shi labari, sai Umar ya ce, masa: “Hakika na san lokacin da Manzon Allah (SAW) ya yi tafiya cikinta (gonar) domin ya sanya mata albarka ne.”
Babi na Goma: Idan mutum ya rika neman tsari daga bashi:
121. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri – Hawwala Sanad- ya ce, “Isma’il ya ba mu labari ya ce, dan uwana ya ba ni labari daga Sulaiman daga Muhammad dan Abu Atik daga dan Shihab daga Urwatu cewa: “Lallai A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ba shi labari cewa: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya kasance yana addu’a a cikin Sallah yana cewa: “Allahumma inni a’uzu bika minal ma’asam wal magram,” sai wani mai magana ya ce, “Me ya sanya Manzon Allah (SAW) ya yawaita neman tsari daga bashi? Ya ce, “Idan mutum bashi ya yi masa yawa, to idan zai yi magana sai ya yi karya, idan ya yi wa’adi zai saba.”
Babi na Goma Sha daya: Sallar gawa ga wanda ya mutum ya bar bashi:
122. An karbo daga Abul Waleed ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari daga Addiyu dan Sabit daga Abu Hazim daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Daga Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya mutu ya bar dukiya to yana ga magadansa. Amma wanda ya bar wani nauyi (bashi) to yana kanmu.”
123. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Abu Amir ya ba mu labari ya ce, Fulaih ya ba mu labari daga Hilal dan Aliyu daga Abdurrahman dan Abu Amratu daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Babu wani mutum mumini face ni ne mafi cancanta da shi a cikin duniya da Lahira, ku karanta in kun so fadar Allah cewa: “Annabi shi ne mafi cancanta da muminai daga rawukansu,” duk wani mumini da ya mutu ya bar dukiya, to na magadansa ne wadanda suke raye. Wanda ya bar bashi ko zuriya marayu, to, lallai ya zo mini ni ne mai jibintarsa.”