Babi na Uku: Wakilta wani a cikin musanyar kudade da awon sikeli. Kuma lallai Umar ya wakilta dan Umar bisa musanyar kudade:
Fassarar Sheikh Is’haq Yunus Almashgool, Bauchi Babi na Uku: Wakilta wani a cikin musanyar kudade da awon sikeli. Kuma lallai Umar ya wakilta dan Umar bisa musanyar kudade: 39. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abdu Humaid dan Suhail dan Abdurrahman dan Aufu. Ya ce, daga Sa’id […]
Fassarar Sheikh Is’haq Yunus
Almashgool, Bauchi
Babi na Uku: Wakilta wani a cikin musanyar kudade da awon sikeli. Kuma lallai Umar ya wakilta dan Umar bisa musanyar kudade:
39. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abdu Humaid dan Suhail dan Abdurrahman dan Aufu. Ya ce, daga Sa’id dan Musayyib daga Abu Sa’idul Khudri da Abu Huraira (Allah Ya yarda da su) cewa: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya wakilta wani mutum bisa dukiyar Khaibara sai ya zo musu da dabinon janib. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Dukkan dabinon Khaira haka suke? Sai ya ce, “A’a, muna karbar sa’i daya na wannan da sa’i biyu, ko sa’i biyu na wannan bisa sa’i uku na waninsa. Sai (Annabi) ya ce, “Kada ka aikata haka, ka sayar da dabinon da ba shi da darajar Dirhami, sa’an nan ka sayo dabinon janid da Dirhamin.” Ya ce, “Haka ma na awon misalinsa.”
Babi na Hudu: Idan makiyayi ko wakili ya ga akuya za ta mutu ko wani abu zai baci sai ya yanka, ko ya gyara abin da ya ji tsoron bacinsa:
40. An karbo daga Is’hak dan Ibrahim ya ce: “Ya ji Mu’atamir ya ce, Ubaidullahi ya ba mu labari daga Nafi’u cewa, lallai shi ya ji dan Ka’ab dan Malik yana ba da labari daga Babansa cewa: Lallai su sun kasance suna da wasu tumaki da suke kiwo a Sal’a (sunan wuri). Sai wata kuyangarmu (baiwa) ta ga wata akuya daga garken tumakinmu za ta mace. Sai ta dauki dutse ta karya ta yanka ta da shi, sai ya ce, musu: Kada ku ci, sai na tambayi Annabi (SAW) ko sai na aika wa Annabi (SAW) wanda zai tambaye shi. Kuma lallai shi ya tambayi Annabi (SAW) game da haka, ko ya ce, ya aika sai (Annabi) ya umurce shi da cin namanta (akuyar).” Ubaidullahi ya ce, “Sai ya ba ni mamaki, cewa ita dai baiwa ce, kuma ita ce, ta yanka.” Abdatu ya karbo daga Ubaidullahi.
Babi na Biyar: Wakilta wanda yake halarce da wanda ba ya halarce ya halatta. Abdullahi dan Amru ya rubuta zuwa ga wakilinsa alhali shi ba ya halarce da ya yi Zakkar Fidiri ga iyalansa yaro da babba:
41. An karbo daga Abu Nu’aim ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Salmata dan Kuhail daga Abu Salmata daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya kasance wani mutum na bin sa bashin rakumi wanda aka san shekarunsa (rakumin). Sai mutumin ya zo domin a biya shi, sai (Annabi) ya ce: “Ku biya shi, sai suka nemi wanda ke da shekarunsa ba su samu ba, face wanda ya fi shi shekaru. Sai (Annabi) ya ce, “Ku ba shi, shi wannan.” Sai mutumin ya ce, “Da dai ka biya wanda ya dace da shekarun rakumina shi ne hakkina har ga Allah, Kai ma Allah zai ba ka hakkinka cikakke.” Sai Annabi (SAW) ya ce, “Hakika fiyayyenku cikin al’umma shi ne wanda idan zai biya wani hakki ya biya shi ta hanyar kyautatawa.”
Babi na Shida: Wakilci cikin neman biyan basussuka.
42. An karbo daga Sulaiman dan Harbu ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari daga Salmata dan Kuhail ya ce, Na ji Abu Salmata dan Abdurrahman ya ce, daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai wani mutum ya zo ga Annabi (SAW) yana neman biyan bashin (rakuminsa) sai ya yi wata kakkausar magana (ta bacin rai). Sai sahabban (Annabi) suka tasar masa kamar za su far masa, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku kyale shi, lallai ma’abucin hakki shi ke da magana.” Sa’an nan ya ce, “Ku ba shi, mai shekaru misalin shekarunsa (rakuminsa). Sai suka ce, “Ya Manzon Allah! Babu kamar nasa face wanda ya fi shekarun nasa,” sai (Annabi) ya ce, “Ku ba shi shi, lallai fiyayyenku cikin mutane shi ne wanda idan zai biya wani hakki ya biya shi ta hanyar kyautatawa.”