Babu abin da APC ta tsinana-Balarabe Musa

Shugaban Jam’iyyar PRP, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya ce Jam’iyyar APC babu abin da ta tsinana, inda ya ce jam’iyyar ta hau mulki ne ta hanyar karairayi da alkawuran da ba za a cika ba. Tsohon gwamnan na Jihar Kaduna, ya yi wannan jawabin ne a lokacin taron Majalisar Zantarwa na Jam’iyyar PRP karo na […]

Babu abin da APC ta tsinana-Balarabe Musa

Shugaban Jam’iyyar PRP, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya ce Jam’iyyar APC babu abin da ta tsinana, inda ya ce jam’iyyar ta hau mulki ne ta hanyar karairayi da alkawuran da ba za a cika ba.

Tsohon gwamnan na Jihar Kaduna, ya yi wannan jawabin ne a lokacin taron Majalisar Zantarwa na Jam’iyyar PRP karo na 54 a Kaduna

Sannan ya ce jam’iyyarsa ta PRP za ta iya magance matsalar idan aka zabe su a zaben 2019.

“Wannan mulkin na Jam’iyyar APC, wadda ta dare karagar mulki ta hanyar karairayi ga matasa da matan Najeriya ta nuna cewa ba ta wani abin a zo a gani sai gare su sai N-Power.

“Maimakon ma gwamnatin ta bullo da sabbin ayyuka, sai dai ma rage ma’aikata teke yi da sunan gyara. Wannan gwamnatin a matakin jiha da tarayya ta nuna cewa ba ta wani abin da za ta yi

Balarabe Musa ya kara da cewa ko a bangaren tsaron ma ba wai ta yi wani baban abu bane.

“A shekara uku da gwamnatin APC ta yi tana mulki. Eh, an ci nasara a kan sansanin Boko Haram da ke Sambisa, amma kuma kungiyar na ci gaba da tayar da kayan baya. Kusan duk mako sai an samu kunar bakin wake musamman a yankin Arewa maso Gabas,” iji shi.