Babu abin da ya hada ni da Gwamnonin G-5 a London —Tinubu

Tinubu ya karyata cewa ya yi ganawar sirri a London da gwamnonin PDP biyar, da aka fi sani da G-5

Babu abin da ya hada ni da Gwamnonin G-5 a London —Tinubu

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya karyata labaran da ke yawo cewa ya yi  ganawar sirri a London da gwamnonin PDP biyar masu korafi, da aka fi sani da G-5.

Tinubu ta bakin kakakinsa, Tunde Rahman ya ce, sabanin abin da kafaren yada labarai ke bazawa, babu abin da ya hada  shi a London da gwamnonin na G-5, wadanda Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, yake jagoranta.

Tinubu wanda ke Kasa Mai Tsarki domin Umrah a halin yanzu, ya ce, “Labaran da ake yadawa tantagaryar kanzon kurege ne mai cike da mugun nufi.”

Kakakin nasa, ya ce, wadanda suka kitsa rahoton kanzon kuregen tare da iyayen gidansu sun yi hakan ne domin cim ma burinsu na siyasa.

Sanarwar ta ce, “Lokacin da Tinubu yake kasar Birtaniya ya lura da wasu labarai da manyan jaridun Najeriya suka yi cewa ya yi ganawar sirri a Lonon da Gwamnonin G-5 daga Jam’iyyar PDP.

“Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC Asiwaju Tinubu, bai damu da wadannan labaran ba, ballantana masu daukar nauyinsa wadanda an riga an san su.

“Ya jajirje kan yakin neman zabe domin samun nasara a zabe shugaban kasa mai zuwa a inuwar Jam’iyyar APC domin aiwatatr da manufar kungiyar da sabunta burinsa ga al’ummarmu a duk bangarorin rayuwa.”

Sai dai ya bayyana cewa yana da ’yancin ganawa da duk wandi dan siyasa da masu ruwa da tsaki da ke da muhimmanci ga yakin neman zabensa da burinsa ga kasarmu da kuma duk wadanda ke bukatar tattauanwa da shi.