Babu abin da zai hana mu zama jam’iyya ɗaya da Kwankwaso — Shekarau

Allah ne Ya ƙaddara cewa da ni da Kwankwaso da Ganduje za mu yi gwamna a Kano.

Babu abin da zai hana mu zama jam’iyya ɗaya da Kwankwaso — Shekarau

Tsohon Gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya musanta cewa akwai wata ƙullaliyar gaba tsakaninsa da takwaransa, Rabi’u Musa Kwankwaso, inda ya bayyana cewa babu ɗaya daga cikinsu da za a iya ɗorawa alhakin saɓanin siyasar da ya shiga tsakaninsu a baya.

Cikin wani bidiyo da karaɗe dandalan sada zumunta, Shekarau ya bayyana cewa rashin jituwar da ke tsakaninsu na siyasa ya samo asali ne daga yanayi da ya fi ƙarfinsu gaba ɗaya.

“Gaskiya ni na yi imanin cewa ni da Kwankwaso ba mu da wata matsala ta zama tare a ƙarƙashin inuwar jam’iyya ɗaya. A duk abubuwan da suka faru, da ni da shi duk babu mai laifi,” inji shi.

Da yake tsokaci kan lokacin da suka yi a jam’iyyun siyasa daban-daban, ya buga misali da yadda Kwankwaso a matsayinsa na Gwamnan Kano ya bi sahun wasu gwamnonin jihohin Sakkwato da Adamawa da Ribas wajen sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.

Sai dai Shekarau ya bayyana cewa shugabannin riƙon kwarya na APC a wancan lokacin da suka haɗa da Bisi Akande, Muhammadu Buhari, da Bola Tinubu, sun kasa tabbatar da adalci a tsarin jam’iyyar.

“A Kano jam’iyyar ANPP ce ta kafa kashi 80 cikin 100 na jam’iyyar APC, amma saboda kasancewar shi [Kwankwaso] gwamna mai ci sai suka ware masa kashi 60 cikin 100 na shugabancin jam’iyyar, wanda muka ɗauki hakan a matsayin rashin adalci,” in ji Shekarau.

Da yake buga wani misalin, Sanata Shekarau ya ce “akwai cin fuska idan ka je sabon gidan da wasu suka gina babu gudunmawarka, ka tarar da mazauna a gidan, sai ka nemi ka yi babakere ta dole sai an ba ka ɗakin da kake so, saboda haka wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. Shi ya sa muka ƙi goyon bayan irin wannan rashin adalci,” inji shi.

Ya ƙara bayar da misali da irin abin da ya faru a jam’iyyar PDP, yana mai cewa “a can ma Kwankwaso ba shi ne abin zargi ba, domin shugabannin jam’iyyar ne suka yanke shawara.”

A cewarsa, “ko wannan batu na rashin adalci da ya taso a jam’iyyar NNPP a yanzu, yana da nasaba ne da watsi da tsarin raba madafun iko da aka amince da shi tun farko.

“Ko a yanzu ni da Kwankwaso mukan zauna mu tattauna kan wasu batutuwa. Ba mu taɓa cewa ba za mu zauna a ƙarƙashin jam’iyya ɗaya ba. Komai yana hannun Allah.

“Shekarau 20 da suka wuce, da wani zai ce maka zan zama gwamna, da ka rantse cewa ba zai yiwu ba saboda abu da mu taɓa tsammani ba—haka shi ma ya ke a wurinsa [Kwankwaso],” in ji Shekarau.

Shekarau ya nanata cewa ƙaddarar Ubangiji ta sanya da shi da Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje duk suka riƙe kujerar Gwamnan Kano “ba don babu waɗanda suka fi mu cancanta sai don haka Allah Ya riga ya rubuta.

“Akwai mutane da yawa da sun fi mu ta kowane fanni na rayuwa, amma Allah Ya zaɓe mu,” in ji Shekarau .

Aminiya ta ruwaito cewa a baya-bayan nan ana ƙoƙarin ganin an haɗa kan manyan ‘yan siyasar Kano —Kwankwaso, Ganduje da Shekarau — domin ci gaban jihar.

Ko a kwanakin tsohon ɗan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Alhaji Abdulsalam Abdulkarim Zaura, wanda aka fi sani da AA Zaura, ya bayyana aniyarsa ta sasanta manyan ‘yan siyasar jihar guda uku.