Babu aure sai da gwajin lafiya a Gombe
Mene ne sunan malamin? Sunana Abdullahi Usman, jami’in sashin gwaje-gwaje a Gidan Magani da ke Gombe. Yaya kuke gudanar da aikin gwaje-gwaje ga mutanen da suke shirin yin aure? Eh, muna ba da shawara ce wajen yin gwaje-gwajen cutar kanjamau da na ciki kuma kyauta ne, amma sauran gwaje-gwajen na rukunin jini (genotype) da ciwon […]

Mene ne sunan malamin?
Sunana Abdullahi Usman, jami’in sashin gwaje-gwaje a Gidan Magani da ke Gombe.
Yaya kuke gudanar da aikin gwaje-gwaje ga mutanen da suke shirin yin aure?
Eh, muna ba da shawara ce wajen yin gwaje-gwajen cutar kanjamau da na ciki kuma kyauta ne, amma sauran gwaje-gwajen na rukunin jini (genotype) da ciwon hanta (hepatitis) da sikila (skil cell), ana biya ne. Kuma mukan gaya wa mutane cewa ya kamata su yi gwaje-gwajen na baya ba sai a lokacin da suka zo gwajin kanjamu ba, saboda yana da kyau don gudun kamuwa da cutar sikila ko ta hanta, domin idan aka gano cutar hanta da wuri ana iya magance ta kafin ta taba koda. Idan suna da ra’ayin hakan wadansu sukan dawo daga baya su yi.
Yaya ake gwajin sikila kuma wadanne nau’o’in jini ne ba a son masu su su yi aure?
Gwajin sikila idan mai kwayar jini na AS da AS suka hadu sukan haifi mai sikila a cikin ’ya’ya hudu da za su haifa. Mai AA kuma zai iya auren mai AA da Ad kuma su ba za su haifi mai sikila ba.
Idan za ku gwada mutane a bangaren kanjamu ya kuke farawa?
Da farko muna fara tambayarsu ko sun san hanyoyin kamuwa da cutar, idan sun sani ko ba su sani ba muna yi musu karin bayani sannan mu tambaye su cewa kun yarda idan aka gwada a fadi amsa a gabanku ko a gaya wa kowa amsarsa daban? Wadansu sukan yarda a fada a gabansu duka, wadansu kuma suna cewa a gaya wa kowa amsarsa daban.
Idan suka yarda a fada a gabansu idan aka samu daya na da kanjamau, daya babu yaya suke yi a gabanku?
Idan suka yarda mu fada a gabansu muna fada wa wanda ba ya da cutar a tsakaninsu mu roke da kardaya tona wa dan uwansa asiri, tunda mu ma ba ma gaya wa kowa. Idan mutum ya yarda mu dora shi a kan magani. Kuma idan wani ya tona asirin wani doka tana aiki a kansa in jami’in lafiya ne ana iya cin tararsa kuma a kore shi daga aiki.
Wanda yake da kanjamau yaya ake yi, yana yin aure ko ba dama ya yi aure?
A lokacin, idan muka samu wanda yake dauke da kanjamau namiji muna iya hada shi da macen da take dauke da kanjamau su yi aure haka in mace ce, sukan yi aure har su haihu kuma dan da za su haifa ya zamo ba ya da cutar. Amma idan za su yi auren muna nunawa a takardarsu ta gwaji cewa ba su dauke da cutar, amma mu mun san suna dauke da ita su ma sun sani. Muna yin haka ne saboda idan babu takardar ba za a yarda a daura musu aure ba, shi ya sa muke yin haka saboda sirri. Idan suka yi auren za su ci gaba da shan maganin kuma za su yi rayuwa mai kyau.
Ta yaya za su haifi dan da ba ya dauke da kanjamu?
Idan suka kiyaye da shan magani kuma suna cin abinci mai kyau da ’ya’yan itatuwa. Shi ma jaririn da suka haifa za a ba shi magani na mako shida kuma ba za a shayar da shi nono ya wuce na shekara daya ba, bayan wata shida sai a sake yi wa jaririn gwaji idan ya
kai wata 18 sai a sake a nan ne za a tabbatar yana dauke da cutar ko babu.
Kamar kashi nawa ake samu na yaran da suke daukar cutar daga iyayensu?
A cikin yara dari bai wuce a samu yaro daya wanda idan ba a kiyaye ba yake kamuwa da cutar sauran 99 suna tsira daga cutar saboda yanzu ana fadakar da iyaye kuma suna kiyayewa.
A bangaren ciki fa yaya ake gwajin kuma ma’aurata suna karbar abin da hannu biyu?
Da farko muna yin gwajin ciki ne bayan na HIb (kanjamau), lokacin da ma’auratan suka zo gare mu saboda (a Musulunci) ba a son mace ta kai wa mutum cikin da ba nasa ba, muna yi nan take muke fada idan saurayin ne ya yi mata muna gaya musu cewa ba aure a tsakaninsu ya bari sai ta haihu idan kuma ba shi ya yi mata ba, to muna gaya masa don ya sani, ta haka muka kubutar da wani malami daga auren wata mai ciki.
Me ya kawo aka fara gwajin ciki tunda an fi yin na kanjamu ne?
Mun fara gwajin ciki ne a shekarar 2016 lokacin da aka yi auren zawarawa a Gombe inda muka samu mata masu ciki fiye da 10. A shekara ta 2017 ma mun samu masu ciki 13 daga shekarar 2016 zuwa 2017 mun samu mata masu ciki 23 ke nan.
Wace shawara kuke bai wa ma’auranta lokacin da aka samu sakamakon da bai yi musu dadi ba?
Wadansu ba sa yarda da amsar da muka ba su suna bijirewa su ce su dole sai sun auri mai lafiya domin ba su yarda da cewa suna da wannan cutar ba, wadansu kuma suna karba da zuciya daya sannan sai mu dora su a kan magani mu ba su shawarwarin da suka dace su rika amfani da su.